{ads}

Technology/hot-posts

Recent posts

View all
*BURI NA*     *EPISODE 1*       NAKHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE)JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI📝📝بسم الله الرحمن الرحيمAbid!Abid !! Abid!!. na jiyo sautin muryar mahaifiya ta daga tsakar gida tana kƙwalamin kira. dam gaba na ya faɗi domin  yadda take kiran kaɗai ya tabbatar min da cewa ta dade tana kiran sunana ba tare da na ji ba balle na amsa.  Hankali na yana kan television ɗn dake palourn mu ina kallon abnda na saba kallo wato ƙwallo, da ƙarfi na amsa yadda zata jiyo ni sannan na miƙe na nufi tsakar gidan, har na kai bakin ƙofa naji ihu daga cikin television ɗn, da sauri na juyo dn ganin abnda yake faruwa, abnda zai baku mamaki shine  tsallen nayi da ƙarfi Ina ihu a ƙofar palourn tare da dunƙule hannu na na doki iska dashi nace "" yesss  yesssss.  bn ankara ba ina cikin murna ta taji saukar duka da wayar tv a baya na, a guje na fice daga palourn nayi tsakar gida ina kuka sakamakon dukan ya shigeni sosai, saidai wani ɓangare na zuciya ta yana yana cike da farin cikin samun nasarar da team dn da nake spoter suka yi wato dai real madrid wanda mukewa laƙabi da gidan madara.Da bulala a hannun mama tayo kaina tana faɗa niko ba abnda nakeyi sai aikin bata haƙuri. ""Ai dama kun saba dk gidan nan idan akaji ihu da kururuwa kece da Abid, menene amfanin yaron da ba zaka more shi ba ƙattin dake buga boll a tv sun  fika mahimmanci a wajansa bayan mudai munsan boll ɗin nan kafurci ce ko da yake yanzu ai zamani ne ba abn mamaki bane mutum ya fice daga musulunci gaba ɗaya,  ai kedai Binta haihuwa batayi miki rana ba dk wannan maganganun kishiyoyin  mama keyi suna  watso mana harara nida mama. zuciyar mama tayi baƙi sosai da sauri ta yadda bulalar ta shige ɗaki, jiki na ba ƙwari na bita cikin ɗakin, a bakin gado na tarar da mama a zaune tana share hawaye,  hankali na ya tashi sosai a hankali na ƙarasa na tsuguna kusa da ƙafar ta nace "" dn Allah mama kiyi hakuri bazan sake kallon boll ba na haƙura dn Allah mama ki dena yi mn kuka malam yace Allah yana fushi da wanda iyayen sa suke fushi da shi,""Murmushi na gani a fuskar mama ta dafa kaina kamar wani abu bai faru ba tace"" Abid ni mahaifiya ce kai kaɗai Allah ya barmin ƴan uwan ka do sun mutu bazan taɓa yin kuka a dalilin ka ba in sha Allah, wannan ma ba kaine ka sani kuka ba ina takaicin jifanka da munanan kalamai da matan gidan nan keyi amma kai babu ruwan ka Abid kaƙi canjawa, ba nida burin yanke maka cikin burin ka saidai koda yaushe ina roƙon ubangiji ya zaɓa maka abnda yafi alkairi a cikin rayuwar ka"" nima murmushin nayi nace"" mama kenan dai boll ba kafurci bane ba ko ? bata bani amsa ba saima kama kunne na da tayi ta murɗa da ɗan ƙarfi saida na saƙi ƙara sannan ta saki dk da naji zafi amma naji daɗin yadda tayi dariyar ƙarar da nayi, haƙiƙa ina tsananin son mama ta dk duniya babu mai kula da rayuwa ta sai ta."" Garin kwaki zaka siyo da sugar kazo kasha kafin lokacin islamiyya"" wani irin zafi naji a zuciya ta na rasa meyasa ake bambanta mahaifiya ta da sauran mata Baba na kllm ana yin girki a gidan mu wata rana harda nama amma nida mama saidai musha kwaki ko ta shanya ƙanzo tayi mana  jaloup ɗn sa mu ci, abnda yake cimn zuciya kenan kuma narasa wanda zai bani amsa tnda mama ba zata faɗa mn ba.Wani ɗaki ne irin ɗakin ƙauye amma a cikin kauyen ma masu rufin asiri ginin bulo ne na ƙasa yasha yaɓe, daga cikin ƙakin wani buhu ne aka shimfiɗa sai wata jaka daga gefe. wata yariya ce wacce ba zata wuce shekara tara ba kwace a ƙasan buhun ta ƙudundune jikin ta alamun jin sanyi ya bayyana a yanayin ta, bacci take sosai da alamun ta saba da yanayin, kamar daga sama taji saukar ruwa a kanta, a matuƙar gigice ta farka jikin ta yana rawa take ja da baya tana kallon matar dake tsaye kanta tana jijjiga jiki.Eeeee lallai kyayi bacci tnda ni ƙanwar uwar kice in dafa in baki kici, tn ɗazu na gama koko amma kina nan kina baccin asara, shegiya muguwa to wllh idan kika sake kokon nan bai ƙareba sai na lahira ya fiki jin dadi shegiya mayya mai suffar aljanu matar ta faɗa tare da jefa wa yarinyar kwanon da ta zubo ruwan sanyin a ciki sannan ta fice tana mita. a hankali yarinyar ta miƙe jikin ta a jiƙe sharkaf tayi tsamo tsamo cikin ruwan, karkarwa kawai takeyi yayin da haƙoran ta na sama ke haɗuwa da na ƙasa. gefen ɗakin ta kalla ta buɗe wata ƴar jaka ta buhu ta ciro wata doguwar rigar atamfa wacce ta koɗe ta fara canja kala ta saka ta zura hijabin ta wanda tsakiyar kan ya fara yagewa  sannan ta fto tsakar gida.robar koko ta ɗauka wacce aka rufe da tire na silver an ɗora ƙananun robobi da ludayin shan kokon a kai.A kanta ta ɗora ta nufi hanyar waje tana jin wani sanyi yana ratsa jikin ta har cikin ƙashin ta.Ruwan da aka kwana anayi yasa hanya ta lalace ƙasa ta jike wajan ba daɗin tafiya haka dai ta dnga lallaɓa wa tana takawa a hankali  hannayen ta rike da robar kokon har ta ƙaraso inda suke zama ita da abokan tallan ta. wajan babu kowa sai ita kaɗai dk da tasan ba wanda zai fto talla yau hakan bai hana ta jin kewar mutane ba Ta wuce awa guda a wajan ba tareda taga giftawar koda mutu ɗaya ba bare a siya abnda take saidawa, ga wani mugun sanyi da bacci da yake addabar ta, ƙudundune hannayen ta tayi cikin hijabin ta ta kwantar da kanta akan guiwar ta nan da nan wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita, ta ɗauki lokaci mai ɗam tsaho tana baccin, kamar an tsikare ta tashi ta ɗago kanta da sauri ta fara sauke manyan fararen idanuwan ta akan robobin zuba kokon dake yashe a gefe guda, sannan ta maida kallon ta ga robar kokon wacce   babu komai s ciki sai alamun an zuba koko a cikin robar ,Da sauri ta miƙe tsaye ta kama dube dube a wajan, bata ga kowa ba cikin kiɗima da tashin hankali tare da bugun zuciya ta tsinci kanta  a zaune dirshan wasu zafafan hawaye na kwaranyowa daga ramin idon ta.
*🌹*RASHIN TABBAS*🌹ByJagabar royal star✍️✍️💪💪*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*        {R.S.W.A}https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu*Page:-11&12__________________Cikin nutsuwarsa yayi picking call d'in tare da kara wayar a kunnansa yayi shuru ba tare da ya ce komai ba, amma fuskan nan tashi d'auke da murmushidaga can 'bangaren Mommynsa da taji shuru, itama se tayi shurun ba tare da tace komai ba amma a saman fuskarta murmushi kawai takeyi, almost 3minute sannan ya bud'e baki a hankali ya furta  ""First love""banza tayi dashi kamar bata ji shi ba, aikuwa cikin shagwa'ba ya kuma cewa ""uhm uhm uhm first love plz say something mana ",daga can 'bangaren ta soma dariya kafin tace"Wallahi my Son baka da kirki har ni zan kira ka atleast 5times amma bakai picking call d'ina ba, sannan kayi picking d'in ma nice kake so na fara yi maka magana?? to sannu isashshe", ta k'arasa maganar tare da zabga harara tamkar yana gabantaduk da da wasa tayi masa k'orafin amma seda yaji wani iri yana k'aunar mahaifiyarsa fiye da kowa da komai dan haka cikin sanyin murya ya ce""am so sorry my first love kiyi hak'uri wallahi 2days nayi busy sosai shiyasa, yanzu kuma da kikaimun misscall bacci nake shiyasa but kiyi hak'uri my happiness", magana yake tamkar baya san yinta, daƙyar yake motsa la'b'bansa Seda ta jira yakai aya sannan tace"'ai shikenan na maka uzuri dama kira nai naji lafiyarka, ya aikin naka??",  ta jefa masa tambayar tare da kai idanunta kan Alhaji Sulaiman wanda ke saukowa daga upstairs jikinsa sanye da riga armless da wando 3q k'afarsa sanye cikin sleepper masu kyan gaskedaga can 'bangaren ya ce""aiki alhmdllh my first love, aiki ya kacamemun, i need ur prayer at any time", "Karka damu addu,a kullum cikin yi maka ita nake yi, Ubangiji yaci gaba da dafa maka a duk abunda kasa a gaba" Cewar mommyn ""amsawa yayi da amin,kafin ya kuma cewa""First love ina Raudha tinda akai bikin shikenan tadena nemana kwata-kwata kuma sometimes Ina kiran layinta but se inji is not available", ya k'arasa maganar tare da zuro k'afafunsa daga saman bed d'in ya zauna sosai a bakin gadontini mommy ta soma in.ina amm...uhm dama   unnmmm "Alhaji Sulaiman ne ya kafeta da ido ganin duk ta dabar barce yasa ya mik'a hannu ya kar'bi wayar tare da kiran sunan shi""IMRAN"jin muryar mahaifinsa yasa shi fad'in"na,am Daddy dama kana kusa da Mom, yanzu nake tambayarta Raudha ta dena nemana Daddy bansan meyasa ba""Kawar da zancen Alhaji Sulaiman yayi,ya shiga tambayarsa ya aikinsa na nantinda mommy ta bashi wayar ta zauna kan kujera 2 seater take ta rusar kuka Imran ya tayar mata da mik'i na rashin Raudha, gashi Mahaifinsa ya hana ta fad'a masa halin da ake ciki na rashin Raudha da suka yiSun jima suna wayar kafin suka yi sallama, zama Alhaji Sulaiman yayi kusa da Mommyn ya tsaya yana kallonta yanda take kuka tamkar wadda akaiwa bushara da wutar jahannama Can yayi ajiyar zuciya yace""haba Hannatu yanzu fa wata d'aya kenan da rasuwar Raudha har yaushe zaki dena wannan kukan, se kace ba musulma ba, Allah ne fa ya bamu ita, kuma shine ya kar'bi kayarsa sa bo da me kike nema kiyiwa Allah butulciaddu,a ita ya kamata kiyi mata bawai kuka ba, tinda ya fara magana ta d'ago jajayen idanunta da suka jajir ta zuba masa su, fuskar nan tayi kaca -kaca da hawaye, daƙyar ta iya bud'a baki ta fara magana""Haba Abban Imran wallahi dole nayi kuka, ko ruk'o aka bani Yarinyar nan irin kisan wulak'ancin da akai mata dole nayi kuka bare kuma ni na haifeta da cikina, sannan na kasa yadda cewa Muhseen ne yayiwa Raudha irin wannan kisan har yanzu wallahi, gashi ka hana a fad'awa Imran Dan me zaka ce kuma na dena kuka??? ni kad'ai nasan rad'ad'in da zuciyata take ciki, wallahi summa tallahi har yanzu nasa aimun secret investigation akan wannan lamarin bazan bar jinin Raudha ya tafi a banza ba, tinda ka hana Imran ya sani ai ni ba zaka hanani abunda duk nai niyyar yi ba",Cikin 'bacin rai duk take wannan maganganun tini Alhaji Sulaiman ya mik'e tsaye  tare da daka mata wata gigitacciyar tsawa yana zare mata idanunsa wad'anda tini sun kad'a sunyi jajir, cikin 'bacin rai ya ce"Hannatu ni kika rufe ido kina fad'awa maganganu san ranki?? sa bo da na miki nasiha!!! lallai kin isa kin tumbatsa, toh kisani muddin na isa dake a yanzu anan wurin ina so ki ajiye maganar kisan da akaima Raudah kamar yanda na umarce ki, Raudha dai "yata ce ba ke kad'ai kika haifeta ba, nayi nawa binciken kuma nakai me laifi court har an yanke masa hukunci dan haka magana ta k'are",Se Kuma ya sassauta muryarsa yaci gaba da cewa"Kiyi hak'uri me hak'uri yana tare da nasara a ko ina, ko kin manta Allah ne yace yana tare da masu hak'uri,dan hk ki kwantar da hankalinki wani irin murmushi gefen baki tayi kafin Kuma da sauri tasa hannu tafara goge hawayenta sannan ta kalle shi tace""Give me my phone"Mik'a mata wayar yayi jiki a sanyaye yace"Toh kiyi murmushi Mana!Murmushi tasaki a k'ok'arinta na danne 'bacin ranta sannan tace Masa""Muje dinning dinner is ready       Tin ranar da Aunty Laura taje gidan Ummu batasake komawa ba, haka kuma bata sake kiransu a waya ba,Ummu ma ta tattarata ta watsar ta zubawa sarautar allah Ido, a gefe guda kuma tana mamakin sauyawar da Laura tayi lokaci guda, amma taci alwashin seta gano dalilin dayasa Laura ta juya musu baya.       ☘️ *PRISON* ☘️Zaune yake ya zuba uban tagumi yayi wata irin muguwar rama ta fitar hankali,yayi bak'i tamkar ba Muhseen d'in nan ba d'an gayu me ji da k'uruciya, sauran "yan d'akin kuwa se sabgoginsu sukeyi masu musu nayi ,masu wasan banza nayi shidai Yana zaune wuri d'aya tunani tamkar ze fasa kwakwalwarsa, tabbas yasan wnn mak'ark'ashiya ce aka shirya masa,Kuma koma su waye tabbas sunyi nasara a kansa,babban abunda yake bashi mamaki yanda bega Aunty Laura ba kwata kwata,batazo ba tinda aka zo aka kamashi,batazo court ba lokacin da ake Shari,ah toh me hakan ke nufi???? yana cikin wannan tunanin ne yaji wani daya cikin "yan d'akin nasu me suna uban zuga  yana cewa""Wannan tunanin baze kaika ko Ina ba yaro kawai kasaki jiki ka fawwalawa Allah ka ka zauna zaman jiran wa,adinka yacika kamar yanda mukai, mu nan daka gan mu duk miyagu ne, mutanan banza ne mu shiyasa ko damuwa banayi da zaman mu a nan wajan, yanzu ma planning muke had'awa ta hanyar da zamu bi mu gudu daga wannan gidan azabaryak'arasa maganar yana wata shashashar dariya da girman sa da komai amma yazama wani soko malohoshidai Muhseen bece masa komai ba,se Ba'ba ne ya kar'bi maganar da cewa""Haba ya zaka kwafsa mana,kawai daga ganin mutum ka Kama kwashe sirrin mu kana fad'a masa idan bakinsa bakin aku ne fa,dallah malam ka yarfass kasawa bakinka sakata,ka kyaleshi idan yaga ze saki jikinsa yasaki idan Kuma baze saki ba shiyasani cannnn ta yagamassshidai Muhseen bece musu komai ba binsu kawai yake da Ido yana nazarin kowanne a cikin su,abunda yadamesa daban sukuma abunda suke tunani daban,yanaso ya tambayesu game da yanda tsarin gidan yake amma ya lura ba mutanan arzik'i bane dan haka yaja bakinsa yayi shuru yana cikin wannan tunanin wani gandiroba yazo bakin k'ofar nasu da wata farar paper a hannunsakallon su yayi d'aya bayan d'aya sannan ya mayar da idanunsa kan takardar,biro yazaro jikin aljihun uniform d'insa ya d'anyi rubutu kan takardar sannan yakuma kallon su yace""Number 52 da number  44 sufito waje,ya k'arasa maganar yana k'ok'arin bud'e k'ofar Tinda sukaji ankira numbobin su suka mik'e tsaye wasu tsoffi ne su buyi Suka fito, dama tinda sukaga wannan gandiroban sun san aikin wahala za,a Sanya su dan shi ganin sa ba alkhaeri bane a fad'arsubayan sun fito yakuma kallon takardar sannan yace""Ina mumber 56 shima yafitoshuru Babu Wanda ya motsa a cikinsu,Muhseen da besan shi ake kiraba ya duk'ufa yanata tunani, shikuwa gandiroban Jin shuru na Wanda yataso yasa shi yakuma kallon takardar yakuma maimaita musu Amma still shuru ba Wanda yataso sema Suka shiga kallon kalloa fusace yace """Wanene Muhseen  Imam Ali??? Yayi tambayar yana kallon su d'aya bayan d'ayada sauri Muhseen yad'ago yazuba masa ido a hankali yamik'e ya tunkari k'ofar tare da cewa "ninewani banzan kallo gandiroban yashiga watsa masa kafin yace""Saboda k rainawa mutane wayo kanaji ana kiranka Amma kayi kunnan uwar shegu da mutane toh idan bakasani b bakasani daga ynzu Kaine number 56 yak'arasa maganar tare da ingizo k'eyar Muhseen gaba ya hankad'osho daga cikin d'akin✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🌹 *RASHIN* *TABBAS* 🌹ByMaryam Naseer Ibraheem (jagabar royal star)*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*        {R.S.W.A}https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu*BISMILLAHIR RAHMANUR RAHIMPage:-9&8::::::::::____________Shiga d'aki tayi ta shirya cikin doguwar riga bak'a anyi mata ado da red stones, rolling d'in mahayafin rigar tayi sannan ta d'auki wayarta tare da zura takalma heel's a kafarta sannan ta d'auki  hand bag d'inta ta fito.Tararwa tayi mai aikin tata har ta kawo mata chieps da slide bread d'aga murya tayi tare da kwala mata kira;Amsawa tayi da sauri ta nufo polourn tana fad'in ""sannu da fitowa Hajiya ai na kawo abincin na tarar kin shiga ciki, shine na ajiye miki akan center table d'in".""Okay ni yanzu fita zanyi kiyi girki kafin na dawo sannan na kira wayar Hubby akashe idan ya dawo ki gaya masa na fita ba jimawa zanyi ba," cewar Aunty Laura ""To Hajiya adawo lafiya Allah ya tsare," Jimmai ce tayi maganar tana mik'ewa tsaye.Bata amsa ba tasa kai ta fita.Tsayawa tayi bakin titi ta fito da wayarta ta soma neman numbern Alhaji Sulaiman, bugu d'aya ya d'auka yana fad'in ""Hajjaju ba dai har kin zo ba?, naga lokacin da muka yi dake da saura bai cika ba". dakatawa yayi dan ya ji amsar da zata bashi.""A'a Alhaji Sulaiman ga ni dai na fito zan taho yanzu haka ma ina bakin titi a tsaye shine nace bari na sanar maka" cewar Aunty Laura ""Ok to yayi sai kin iso, ina jiranki," sallama su ka yi ya ajiye wayar.After some minute tak'arasa guest house d'in Alhaji sulaiman lokacin shi bai zo ba sai da ta zauna jiransa.Gida ne babba mai girman gaske komai na more rayuwa akwai shi a gidan nan, bene ne hawa uku babu Wanda zai kalli gidan nan yayi zaton ba mata a cikinsa, domin kuwa komai akwai har masu aiki wad'an da suke masa aiki a k'alla sun kai wajan mutum ashirin, gidan yana da gate guda biyu daya k'ofar tana ta gaban gidan ne yayin da d'ayar kuma take a bayan gidan, ta gaban gidan ce kawai akwai masu gadi a wajan amma wadda take a bayan gidan wasu karnuka ne rik'ak'k'un gaske suke gadinta. Hawa na farko anan Alhaji Sulaiman yake ganawa da bak'insa na musamman hawa na biyu dana ukun kuma babu wanda ya ta'ba zuwa wurin, shi kad'ai ne yake zuwa bayan shi kuma sai wani amininsa Alhaji Hadi wanda da alama y yarda dashi sosai.Zama tayi a falon k'asa tana jiran zuwan Alhaji Sulaiman kafin kace wannan tini ma'aikatan gidan sun cika mata gabanta da abubuwan ci dana sha kala daban-daban.Bata yiwa kanta kwauro ba haka ta duba abunda zata iya ci fried rice ta zuba wadda tasha kayan lambu da yankakkiyar hanta sannan ta zuba soyayen naman zabi jar suya tasoma ci dan dama da yunwa ta fito.Har ta gama cin abincin ta tsiyaya lemon chivita ta kora dashi, wayarta ta jawo domin takira Alhaji Sulaiman taji ko ya taho.Tana kiranshi yana shigowa falon tare da fad'in ""Hajjaju Laura kiyi hak'uri fa na zaunar dake kin san abubuwan ne dayawa" yana magana yana nufo cikin falon hannunsa rik'e da briefcase yana k'ara gyara zaman babbar rigar jikinsaMurmushi Aunty Laura tayi sannan tace ""ba komai Alhaji" tak'arasa maganar tana me kare Masa kallo yanda taga yanata zabga murmushi.""To ya gida Ina fatan komai lafiya Alhaji Sulaiman ne yayi maganar yana kallon Aunty Laura bayan ya zauna""Alhmdllh Alhaji ya Kuma mu kaji da jimamun wannan abu daya faru?" cewar Aunty Laura tayi maganar tana kara gyara zamantaWani k'ayataccen murmushi Alhaji Sulaiman yasaki kafin Kuma yasoma dariya,ita dai tsayawa tayi tazuba masa ido sai da ya gama dariya sannan ya dubetaMadadin ya amsa mata maganarta sai cewa yayi"Laura jimami ai ku za'a tambaya ni wane jimami zanyi ai na had'a duka na bar muku ya k'arasa maganar yana kallon Laura, yayi hakan ne dan yanaso yaga reaction d'inta.Abun mamaki sai yaga ita ma ta fara dariya k'asa-k'asa mara sauti seda tagama sannan tace""Nima Kam ai ba za'a tambayeni jimami ba, dan bai shafeni ba masu yi dai suna can sunayi tak'arasa maganar tare da ta'be bakinta tana yatsina fuskaSosai suka tattauna da Alhaji Sulaiman akan abunda suka shiryawa Muhseen sannan Alhaji Sulaiman yakuma cemata""Laura kema fa dan baki ta'ba haihuwa bane, amma wallahi wannan harkar tamu itace ta kamace ki, zakiyi kud'i zakiyi suna a duniya,zaki mallaki komai da kike burinsa a rayuwaTunda ya fara magana tayi shuru tana kallonsa gaba daya ya gama kwad'aita mata dad'in kud'i, har yasa ta fara wani tunani, jin tayi shuru bata tanka Masa ba gashi ta kafeshi da idanuwa da alama tayi zurfi a tunanintaYatsunsa biyu yasa ya Murza Suka bada sautin d'assss a take ta yi firgigit tadawo hayyacinta,""Tunanin me kikeyi ne haka Laura??? Alhaji Sulaiman ya tambayeta""Alhaji ina nazarin maganganunka ne zan zauna a tsanake nayi tunani akansu in Sha allah tak'arasa maganar tana mik'ewa tsaye.""yanzu ni zan wuce, gidan su Muhseen d'in ma zanje dan sun isheni da masifar Kira wlh Kamar mayu idan banje ba zasu iya kawo wani abun a ransu tana magana tana yatsina fuska daga k'arshe ma taja dogon tsaki""Shi ma mik'ewa tsaye yayi yana fad'in "ai ya kamata ki je d'in dama kar suyi zargin wani abu, ki kula sosai kar kiyi wani Abu da zai sa su gano ki" cewar Alhaji Sulaiman.Rungume hannunta tayi saman k'irjinta tana murmushi sannan tace""Alhaji kenan ta yaya zan bari su gane!??? ai kaima kasan ba zai yuwu ba, yanzu dai ina kamasho dan naji bakaimun maganarsu ba, kuma yakamata ace ka mik'omun su.Sosai Alhaji Sulaiman yakama dariya tana kallonsa seda ya tsagaita sannan yace""Laura manya kedai kud'i kud'i kawai Kika sani okay karki damu muje na saukeki tinda nima ba Zama zanyi ba kud'in ki suna cikin mota se nabakiItama dariyar tayi sannan tanufi k'ofar fita daga falon tana cewa""Ai ka fini san kud'i wallahi kai da zaka iya komai akan kudi ciki kuwa har da halaka 'yarka ta cikinka kaga kuwa ai san kud'ina da naka ba d'aya ba ne"Sai da Alhaji Sulaiman yaji gabansa yayi muguwar fad'uwa jin abunda Laura tace amma sai ya dake ya basar.A tare suka fito daga falon habu direbansa yana ganinsa ya taso da sassarfa ya nufi motar dan ya tasheta Dakatar dashi Alhaji Sulaiman yayi tare da cewa""Bani key din ni zanyi driving din but yanzu zan dawo kaje ka huta abunka.Da sauri Habu ya mik'a masa key din motar tashi jibgegiyar gaske kirar land cruiser yana fad'in""To Alhaji adawo lafiya.Amsawa yayi da "Amin" sannan ya zagaya ya zauna a driver seat seda yayi revers ya fito da motar sannan Aunty Laura taje ta bude front seat tazauna a ranta tana cewa""Wannan mota aljannar duniya waiiiiiiiii gaskiya kud'i sunyi a rayuwa. Horn yayiwa mai gadin da gudu ya taso ya bud'e masa tafkeken gate d'in sai da yasa kai zai fice sannan ya tsaya ya kalli mai gadin fuskarsa a d'aure yace""Malam Sule wallahi ba dan kana takwarana ba da tini na sallameka, wai kana gani zan fita amma ba za ka taso ka bud'emun k'ofa ba sai nayita danna maka horn ko??" ya tambaye shi tare da Jan tsaki.Jikin mal. Sule har ya fara rawa yace""Dan Allah Alhaji kayi hak'uri za,a gyara in sha allah, ayi hak'uri ya k'arasa maganar yana rissinawa sannan ya ci gaba ""Hajiya dan Allah a kara bashi hak'uri in Sha allah za'a kiyaye daga yau"Banza Alhaji Sulaiman yayi masa ya kuma sa Kai ya fice da motarsa da gudun gaske. Sai da ya hau titi sosai sannan yajuyo yakalli Laura wadda ta lumshe idanunta tana shak'ar sanyin a.c din motar.Murmushi yayi sannan ya furta""Ga k'oshi ga kwananan yunwa.Bud'e idanunta tayi takalleshi sannan tace""Ban gane ba????"Dariya ya d'an yi sannan yace mata;""Ki shigo kawai adama dake hajiyata kiyi kud'i ki huta". Aunty Laura dai kallonsa kawai take can dai tace. ""Ka bani nan da 2weeks I will think about it".Sannan ta juyar da kanta tana kallon gefen titi tacikin tintec d'in motar.""Kin ce gidansu Muhseen kika nufa ko?" Ya jefo mota tambayar yana k'ok'arin hawa titin da zai sadashi da gidansu Muhseen direct.""Eh amma ka ajiyeni nesa da gidan cox banaso wani ya ganmu tare" tayi maganar tana nuna masa dai dai in da zai ajiyeta .Sai da yayi parking sannan yace ""to kyan alk'awari cikawa inji hausawa".Ita dai ba ta ce masa komai ba sedai binsa da Ido da takeyi.Fitowa yayi daga cikin motar ya bud'e both wata k'atuwar jaka ya d'auko sannan ya dawo ya bud'e motar ya shiga.Mik'awa Aunty Laura jakar yayi yana murmushi.Kar'ba tayi tana kallonsa dan tanaso taji k'arin bayani.Murmushi ya sakar mata sannan yace;""Hajiya Laura wannan jakar da duk abunda ke cikin ta naki ne 6million dollers ne a ciki tukwaicin kine saboda kin bani had'in kai sosai".a razane Aunty Laura ta juyo tana kallonsa ta zazzaro idanuwa bakinta har rawa ya ke yi wajen cewa.""Alhaji 6 million dollars fa kace bama nera ba, kuma duk nawa ne???" kafin ya bata amsa ta ci gaba da cewa."Haba! haba!! wlh kud'in nan sun yi yawa, yanzu idan na fita da jakar nan na shiga da ita gidansu Muhseen ai zasuyi zargin wani abu".kallonta kawai yake yana murmushi sai da ya bari takai k'arshen maganar ta sannan yace;"Idan Kika shigo harkar mu kika h'ada hannu dani wannan kud'in da kike gani ba komai bane Zaki samu ninkin su sau ba adadi, karki damu na baki su kyauta ne saboda yanda Nima Kika bani goyan baya sannan idan kika shiga dasu gidan nan suka tambaye ki na waye kawai kice musu kawarki ce ta turo dasu daga Saudia za'a tsaran mata kaya daga haka kija bakinki kiyi shuru".Ajiyar zuciya Aunty Laura ta sauk'e kafin ta shiga yi masa godiya.D'aga Mata hannu yayi alamar Babu damuwa.Sannan yace.""Ni dai burina KI HADA HANNU DANI.Ba tace komai ba ta bud'e k'ofar motar ta fito hannunta rik'e da k'atuwar jakar da kyar ma ta d'auketa sabida nauyi.Sai da ta kalli ko Ina taga ba yawan jama'a sannan ta soma tafiya Alhaji Sulaiman ma motarsa yayi key ya juya ya bar wajan yana ta sakin murmushi me ma'anoni daban daban.      *Scotland*a round 10:30am dank'areran agogon bangon dake manne jikin bangon d'akin ya buga, wayarsa dake saman side drower ce ta soma ringing, almost 5 times wayar tana ringing amma sam ya kasa motsawa bare yayi picking call d'in.wani Kiran ne ya koma shigowa cikin wayar tashi a hankali ya yaye duvet d'in daya rufa dashi sannan ya yunk'ura ya mik'e zaune yana  k'ok'arin d'aukan wayar kiran ya katse, d'aukar wayar yayi yana kallon screen d'in ganin me kiran nashi yasa shi sakin wani kyakkyawan murmushi✍️✍️✍️✍️✍️✍️
💕💞 *SO KENAN* 💕💞13-14JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI        NAKHADIJA UMAR ABDULLAHI GARKUWAR JARUMAI CE 💪🏽بسم الله الرحمن الرحيمDa sallama Nusaiba ta ƙarasa kusa da kujerar Sahal ta ɗan rusuna ta kalli fuskar sa wacce take a hade kmr an aiko masa da mazon mutuwa, tsuguna wa tayi tare da kama kunnuwan ta da da hannayen ta ce "'""" I'm sorry boss "" yanda tayi maganar tana kwaɓe baki kmar zatayi kuka yasa Sahal sakin wata dariya wacce shi kansa baisan rabon sa da yin ta ba, galala Nusaiba ta saki baki tana kallon yanda yake dariyar ba ƙaramin kyau yayi mata  wani so da kunar sa suna  ƙara fizgar ta.sai da yayi dariya sosai sannan ya tsaya yana kallon yanda ta kafe shi da ido, gira ɗaya ya ɗaga mata tare da hura mata iskar bakin sa a hankali yace ""yane?"", jiki ba ƙwari Nusaiba ta tashi ta zauna a kujerar  dake fuskantar sa tace "" gogiya da yabo su tabbata ga mahaliccin kyau da kyawawa  sannan jinjina ga kyawawan da suke ɓoye kyawun da Allah ya basu ta karasa maganar tana murguɗa masa baki .Waro Ido Sahal yayi ganin yanda Nusaiba ta murguɗa masa ki ita kuma ganin hakan yasa ta turo ɗan ƙaramin bakin ta alamar shagwaɓa, komawa da baya Sahal yayi ya jingina da jikin kujerar da yake kai ya ɗaga kansa sama tare da lumshe idanuwan sa kmar mai bacci daga bisa ni ya huro iska daga bakin sa, soyayya da kaunar Nusaiba suna ƙara azalzala masa zuciyar sa  yana jin ta a dukkan gaɓɓan jikin sa, a hankali ya buɗe idanun sa ya buɗe su tarr a kan ta can cikin makoshi ya furta "" ina kika tsaya kika barni ina jiran ganin ganin matar yarima? yanda y faɗi magnar yana kallon ta yasa Nusaiba ƙara buɗe idanun ta don ta tabbatar da cewa yarima ne kodai mafarki takeyi?Sai da ta tabbatr ba mafarki take yi ba sannan ta bude bakin ta cikin wata zazzaƙar murya tace "" na tsaya zaɓen kayan da zai burge yarima ban sani ba ko zan na burge shi, yanda tayi maganar da sigar abn tausayi ya ƙara bawa yarima dry dn murmushi yayi sannan y nuna mata kujerar dake gefen sa, ba tare da wata mgana ba Nusaiba ta mike tsaye ta zauna kan kujerar tana kallon yanda fuskar yarima ke cike da annuri .Matsowa yayi daga kujerar ƙafafuwan su suna gogar na juna ya dube ta yace "" kin barni cikin matsanancin duhu " da mamaki Nusaiba ta kallon Sahal tace "" my prince nan fa ba dare bane me ya kawo duhu kuma ? Ajiyar zuciya Sahal ya sauke yace yakike tnanin wunin da rana bata fitowa ? Zai kasance cikin duhu har sai dare yayi lokacin futowar wata sannan a samu haske cewar Nusaiba har yanzu tana mamakin kalaman Sahal. bata ƙara mamaki ba saida taji tana cewa ""kece rana ta idan kika ki ftowa zan kasance cikin duhu harsai kinzo kin haska ni" kwabe baki Nusaiba tayi tace "" aa nidai ban yadda ba kai jarumi ne zaka iya jure rashin ftowar rana nikuwa dare ce bazan iya jure rashin ftowar wata ba nidai ka dnga fitowa kana haska ni kar mutanen dake kusa da ni su dnga tsorata. murmushin gefen vbaki Sahal yayi sannan yace "" a nan dai kece jarumar  ni zuciya ta kmr ƙwai take kaɗan take jira ta fashe"". yanda yayi mganar da sigar shagwaɓa ya bawa nusiba dry sosai tayi dry tana jin wani farin ciki sosai a ranta tana godewa Allah daya nuna mata irin son da yarima yake mata  tn kafin Fulanin gobir ta jefa ta cikin musiba. yanayin dariyar da Nusaiba takeyi yasa Sahal jin wani yarr ajikin sa tnda ga ƙwaƙwalwar sa har ƴan yatsun ƙafar sa, komawa yayi ya jingina da kujerar ya lumshe idon sa yana sauraren abnda zuciyar ke fada masa .ALHAMDULILLAHSuhail yaji sauki sosai an sallame shi daga asbti haka suka dawo gida, ranar da suka dawo maryama ta sanar da khadija rashin lafiyar Sahal , da yamma suka fito makaranta suka wuce gidan su Suhail. da sallama suka shiga suka samu Suhail zaune kan tabarma yana shan kunu ,yanda ya rame yayi baki ba karamin tada hankalin khadija yayi ba a hankali ta matso kusa dashi ya kalle shi cike da tausaya wa tace sannu ya jikin? dn guntun murmushi yayi wanda ya ƙara jefa zuciyar khadija cikin masifaffiyar soyayyar sa yace ""jiki da sauki  dama ina so inyi magana dake"", gyara zama  khadija tayi ta sunkuyar da kanta kasa ta sauraron Suhail shima ƙara jingina yayi da bango ya fara magana"" hakika khadija kin cancan ci samun kowace irin soyayya dk da kasancewa ta mutum mara tarbiyya baki guje ni ba baki ƙyamace ni ba dk da irin abnda nake miki baisa kinyi fushi ba, na yadda cewa soyayyar ki ta gaskiya ce kmar wacce nake miki.da sauki khadija ta dago kanta ta kalli Suhail cike da mamakin kalaman sa, ɗaga mata kai yayi alamar tabbatar wa, wani ƙayataccen murmushi khadija ta saki tare da dafe saitin zuciyar ta. Suhail ya cigaba da cewa soyayyar gaskiya nake miki shiyasa banaso ki kasance tare da ni, wani irin bugu kirjin khadija yayi nan take idon ta ya fara kawo ruwa Suhail ya kauda kansa gefe yace khadija ke yar asali ce mai hankali mai tarbiyya zanso ko samu miji na gari ba kmar ni ba sannan bayan wannan ma ni yanzu na kashe rayuwa ta da kaina gaba daya ƙodoji na sun lalace khadija zanyi miki fatan alkairi da miji na garin da zaki samu har zuwa numfashi na na karshe, ina so kawai ki sani ni Suhail ban taba ƙin ki ba ina matukar son ki sai dai nasan ba wanda zai bari ki aure ni, ni kaina idan na ce zan kasance mijin ki banyi miki adalci ba.Girgiza kai khadija ta shiga yi wasu zafafan  hawaye na yawo akan kumatun ta dakyar ta buɗe baki tace "" ni kai nake so ba asali ko wata kamala  ba, kaji tausayi na Suhail kar ka juyar da kyautar da nayi maka, bazan iya jure rashin ka ba, dk abnda khadija take fala ƙaa azalzala wutar son ta take a zuciyar Suhail amma baze iya auren ta ba yana so ta samu rayuwa mai kyau, har ta gaji ta tashi ta riƙe hannun maryama suka juya har ta kai kusa da soro ta tsaya cak ba tare da ta juyo ba tace ""Suhail nasan dalilin ƙin karɓar soyayya ta nasan banyi maka ba a matsayin mata, baka so na, amma ina so ka sani ina son ka kuma zan cigaba da son ka har ƙarshen numfashi na tana gama faɗar haka ta fice da sauri.Dk abnda suka tattauna inna tana ciki taji komai hawaye sosai take yi tana jin dama tana da yanda zatayi da ta haɗa auren Suhail da Khadija Amma babu dama, tasan babu wani uba da zai bawa Suhail ƴar sa bare kuma khadija marainiya ce tana bukatar kyakykyawar rayuwa  gashi Suhailun ta ko abnyi bashida da shi.ƙuna sosai zuciyar Suhail keyi a fili ya furta taƙi fahimta ta, har yanzu bata yadda ina son ta ba Ya ilahi ya furta a hankali yana dafe kansa da hannun sa .Can kuma ya miƙe ya tashi ya shige ɗakin sa, dube dube ya shiga yi a ɗakin har ya gano kwalin sigari aiko ya zauna ya fara sha yana huro hayakin ta hanci ta baki, ya sha guda biyar ya kunna ta shida tari mai ƴarfi ya taso masa nan da nan ya fara fita daga hayyacin sa kafin wani lokaci jini ya fara fitowa ta hancin sa da bakin saOUM SHARIFAT CE .....
🌹 *RASHIN TABBAS*🌹ByMaryam Naseer Ibraheem (jagabar royal star)Plz don,t forget to follow my tiktok account,,,,,👉👉👉👉 *okteety* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*        {R.S.W.A}Ahttps://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu*BISMILLAHIR RAHMANUR RAHIMPage:-7&8:::::::::__________Tinda su Ummu suka dawo gida maƙwafta suke ta shigowa jajanta mata, Ummun su Muhseen mace ce data iya mu'amala tasan darajar mutane, kuma tana zaune da kowa lafiya hakan ne yasa ta sami sheda me kyau a wajan mutanan unguwar tasu,dangin Ummun Muhseen dana Abbansa duk sun zo sun mata jaje tin safe gidan yake cika da mutane, Aunty Laura k'anwar Ummun su Muhseen ce ita take binta, tinda taji labarin abinda ya faru da Muhseen bata zo tayiwa Ummun su Muhseen jaje ba, abunda yabawa kowa mamaki kasancewar Aunty Laura ita ta yaye Muhseen kuma tin daga yaye tace dan Allah abar mata shi dan ita bata ta'ba haihuwa ba, hakan ne yasa Abban su Muhseen yayi kara ya ce yabar mata shi,badan yaso hakan ba sedan yaga yanda take nuna soyayya da kulawa akan Muhseen, duk da kasancewar shima yana tsananin buk'atar d'anshi a kusa dashi dan Muhseen mutum ne me shiga rai tin yana k'arami, amma haka ya damk'awa Aunty Laura shi. tin faruwar wannan lamari rashin zuwan Aunty Laura ya bawa kowa mamaki, abun ya d'aurewa kowa kai ace Muhseen ne ya shiga wannan halin amma ko sau d'aya ba'aga k'afar Aunty Laura ba, kuma tana gari ba wani wajan taje ba.Zainab ce ta kasa hak'uri ta matso kusa da Ummun tasu tace "Ummu wai dan Allah meyasa har yanzu Aunty Laura ko sau d'aya ba tazo ba, ni nayi zaton ma a court d'in zamu je mu sameta na dinga baza ido amma ko me kama da ita ban gani ba ko Auncle   Safyan ne ya hanata zuwa?", ta k'arasa maganar tare da zubawa Umman tasu idanu,girgiza kai tayi sannan tace "wallahi Zainab nima bansan meyasa Laura ba tazo ba, kuma ko a waya bata nemeni ba nayi mamaki sosai amma kirata a waya ki had'ani da ita naji meke faruwa", "toh", Zainab tace sannan ta mik'e ta shiga palourn su wanda Aysha ta gama gyarawa yanzu.fitowa tayi hannunta d'auke da wayar Ummun tasu kusa da ita ta dawo ta zauna sannan ta shiga neman number d'in Aunty Laura,seda ta kira kusan three miscall amma ba'ayi picking call d'in ba kallon Umman su tayi tace "Ummu na kira kusan sau 3 amma bata d'aga ba anya lafiya kuwa?? kodai nakira Uncle Safyan d'in naji??"tak'arasa maganar tana danna wayar ta shiga neman layin Uncle d'in nasu,dakatar da ita Ummu tayi tare da cewa "karki kira shi kitayar masa da hankali ki k'ara kiranta ko za'a dace ta d'auka idan kuma bata d'aga ba ki kyaleta zuwa dare mugani ko zata kira". "Toh", Zainab tace sannan ta k'ara dannawa Aunty Laura kiraLokacin da Alhaji Sulaiman yaja motarsa yabar harabar court d'in kai tsaye gidansa ya nufa dake shagari quarters, shigarsa kenan harabar gidan sa bayan me gadin ya bud'e masa get fitowa yayi yana gyara zaman babbar rigar dake jikinsa wayarsa ta fara ruri,duba me kiran nashi yayi a take ya saki murmushi tare da yin picking ya kara wayar a kunnansa sannan yace  "yanzu nake shirin kiranki dan ina san had'uwa dake urgent kinsan yau nayi zaton zaki zo wajan Shari'ar nan amma ba k'aramun dad'i naji ba da naga banganki ba yanzu yaza'ai ina san ganinki akwai abunda zamu tattauna mushawo kansa",daga can d'angaren ta sauk'e numfashi tare da cewa  "Alhaji Sulaiman kenan nifa wallahi ina cikin firgici da tsoro tinda naga hukuncin da aka yankewa Muhseen jikina yayi sanyi na rasa meyake yimun daɗi wlh, amma dai yanzu kana ina nazo na sameka??", shuru tayi tana jiran me zece,dariya yayi sosai sannan yace "haba dan Allah karki bani kunya mana! toh menene zesa jikinki yayi sanyi,mak'udan kud'in da kike nema kinsame su har ma sun ninnika yanda kika nema, kuma batare da kinyi wani aiki me wahala ba dan haka kisaki jikinki hajiya aci gaba da buga harka kawai",dariya sosai itama tayi sannan tace  "tohm shikenan Alhaji Sulaiman yanzu kana ina nazo nasameka?","Shigowata kenan gida, dan na gaji zan d'an watsa ruwa around 5:00pm kisameni a guest house d'ina",  cewar Alhaji Sulaiman"ok tohm shikenan in Sha Allah zanzo", tana gama fad'ar hakan ta yanke wayar tare da ajiyeta ta mik'e ta shiga bedroom d'inta tana ta zabga murmushi,bayan wasu mintuna da basu gaza arba'in ba ta fito, fridge ta bud'e ta ciro madarar hollandia me sanyin gaske zubawa tayi a cikin glass cup ta koma saman sofa ta zauna tare da kwalawa me aikinta kira Jumma dake kitchen tana mopping tajiyo kiran, da sauri ta ajiye mopper d'in ta fito tana fad'in "ranki yadad'e gani"yawwa Jummai dan Allah kid'an sama mun abu me sauk'i wanda zanci dan yunwa nakeji tafad'a tare da kai kallonta wurin da wayarta take a ajiye saboda ganin takawo haske"toh ranki yadad'e, Jummai tafad'a tare da juyawa zata fita"mik'omun wayata tajiyo muryar uwar d'akin nata tafad'adawowa tayi ta d'auki wayar ta mik'a mata sannan tafita5 miscall tagani na Umman su Muhseen seda gabanta yafad'i amma tadake tare da bin kiranlokacin da kiran yashiga Zainab ce ta shirin d'agawa amma Ummu ta dakatar da ita tare da cewa "bani nayi mata maganaba musu Zainab ta mik'a mata wayarPicking tayi tare da sallama d'auke a bakinta""Wa, alaikis Salam Aunty Laura ta fad'a tare da ajiye cup of hollandia dake hannunta sannan taci gaba da cewa""barka da wannan lokaci Aunty dafatan mun wuni lafiyaUmmun Muhseen bata saurari gaisuwar Aunty Laura ba taceLaura yanzu kin kyauta kenan???? Muhseen fa akaina sharri aka kamashi da lefin da be aikata ba aka yanke masa hukunci na zalinci amma ko sau d'aya bakizo gidan nan ba Laura!!! se mijinki shi dayake ma ba d'an uwana ba shine keta zarya yazo nan gidan yaje court d'in da ake Shari,ar  amma Banda ke!!; a tunanina ma ai kece gaba gaba a wannan lamarin amma se naga kin nad'e hannunki shuru Aunty Laura tayi tana sauraron yayarta ta bata katseta ba har se da takai aya sannan tace""Kiyi hak'uri Aunty wlh dama yau nace zanzo wasu uzurirrika ne suka hanani zuwa amma in sha  Allah yau zanzo mamaki ne yakamaUmman Muhseen jin abinda k'anwar tata tace, kenan har akwai uzurin dayafi tazo taji yaya halin da ake ciki??""jinjina kai Ummu tayi sannan tace ""gaskiya nayi mamaki Laura dama akwai uzurin dakike dashi dayafi wannan?? Muhseen fa d'anki ne ke kika raineshi ya girma tare dake yashak'u dake amma yanzu dan jarabtar ubangiji tabiyo ta kansa shine har zaki bud'a baki kicemun wai uziri ne ya hanaki zuwa! tak'arasa maganar tare dayin shuru taji me Laura zatace""Kiyi hak'uri Aunty Ummu in sha Allah yau d'in nan zanzo,kamar yanda nafad'a miki abubuwa ne sukaimun yawa wallahi, amma tinda nace zanzo ai magana ta wuce ko??ta k'arasa maganar tare da jefa mata tambaya"""Hmmmm Laura kenan shikenan Allah yakawoki Ummu tana gama fad'ar hakan takashe wayar tana duban Zainab data cika famm tamkar zata fashe dan takaici, Aunty Laura tabata mamaki wlh Kuma ba k'aramun haushinta taji ba""gsky Ummu wlh aunty Laura bata kyauta ba sam,ko batazo dan kowa ba ai zatazo dan   Yaya Muhseen""toh Zainab yazanyi da ita kinajin dai abunda tafad'a sedai kawai mu kyaleta kowa yagyara yasani haka ma kowa ya 'bata yasania 'bangaren Laura kuwa jin Ummu ta yanke wayar yasata ta'be baki tare da cewa   ""bani nakar zoman ba rataya aka bani, matsalarki ce batawa ba Muhseen d'in banza, kud'i nafiso fiye dashihaka taita banbamin fad'anta ita kad'ai✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️