🌹 *RASHIN TABBAS*🌹ByMaryam Naseer Ibraheem (jagabar royal star)Plz don,t forget to follow my tiktok account,,,,,👉👉👉👉 *okteety* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A}Ahttps://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu*BISMILLAHIR RAHMANUR RAHIMPage:-7&8:::::::::__________Tinda su Ummu suka dawo gida maƙwafta suke ta shigowa jajanta mata, Ummun su Muhseen mace ce data iya mu'amala tasan darajar mutane, kuma tana zaune da kowa lafiya hakan ne yasa ta sami sheda me kyau a wajan mutanan unguwar tasu,dangin Ummun Muhseen dana Abbansa duk sun zo sun mata jaje tin safe gidan yake cika da mutane, Aunty Laura k'anwar Ummun su Muhseen ce ita take binta, tinda taji labarin abinda ya faru da Muhseen bata zo tayiwa Ummun su Muhseen jaje ba, abunda yabawa kowa mamaki kasancewar Aunty Laura ita ta yaye Muhseen kuma tin daga yaye tace dan Allah abar mata shi dan ita bata ta'ba haihuwa ba, hakan ne yasa Abban su Muhseen yayi kara ya ce yabar mata shi,badan yaso hakan ba sedan yaga yanda take nuna soyayya da kulawa akan Muhseen, duk da kasancewar shima yana tsananin buk'atar d'anshi a kusa dashi dan Muhseen mutum ne me shiga rai tin yana k'arami, amma haka ya damk'awa Aunty Laura shi. tin faruwar wannan lamari rashin zuwan Aunty Laura ya bawa kowa mamaki, abun ya d'aurewa kowa kai ace Muhseen ne ya shiga wannan halin amma ko sau d'aya ba'aga k'afar Aunty Laura ba, kuma tana gari ba wani wajan taje ba.Zainab ce ta kasa hak'uri ta matso kusa da Ummun tasu tace "Ummu wai dan Allah meyasa har yanzu Aunty Laura ko sau d'aya ba tazo ba, ni nayi zaton ma a court d'in zamu je mu sameta na dinga baza ido amma ko me kama da ita ban gani ba ko Auncle Safyan ne ya hanata zuwa?", ta k'arasa maganar tare da zubawa Umman tasu idanu,girgiza kai tayi sannan tace "wallahi Zainab nima bansan meyasa Laura ba tazo ba, kuma ko a waya bata nemeni ba nayi mamaki sosai amma kirata a waya ki had'ani da ita naji meke faruwa", "toh", Zainab tace sannan ta mik'e ta shiga palourn su wanda Aysha ta gama gyarawa yanzu.fitowa tayi hannunta d'auke da wayar Ummun tasu kusa da ita ta dawo ta zauna sannan ta shiga neman number d'in Aunty Laura,seda ta kira kusan three miscall amma ba'ayi picking call d'in ba kallon Umman su tayi tace "Ummu na kira kusan sau 3 amma bata d'aga ba anya lafiya kuwa?? kodai nakira Uncle Safyan d'in naji??"tak'arasa maganar tana danna wayar ta shiga neman layin Uncle d'in nasu,dakatar da ita Ummu tayi tare da cewa "karki kira shi kitayar masa da hankali ki k'ara kiranta ko za'a dace ta d'auka idan kuma bata d'aga ba ki kyaleta zuwa dare mugani ko zata kira". "Toh", Zainab tace sannan ta k'ara dannawa Aunty Laura kiraLokacin da Alhaji Sulaiman yaja motarsa yabar harabar court d'in kai tsaye gidansa ya nufa dake shagari quarters, shigarsa kenan harabar gidan sa bayan me gadin ya bud'e masa get fitowa yayi yana gyara zaman babbar rigar dake jikinsa wayarsa ta fara ruri,duba me kiran nashi yayi a take ya saki murmushi tare da yin picking ya kara wayar a kunnansa sannan yace "yanzu nake shirin kiranki dan ina san had'uwa dake urgent kinsan yau nayi zaton zaki zo wajan Shari'ar nan amma ba k'aramun dad'i naji ba da naga banganki ba yanzu yaza'ai ina san ganinki akwai abunda zamu tattauna mushawo kansa",daga can d'angaren ta sauk'e numfashi tare da cewa "Alhaji Sulaiman kenan nifa wallahi ina cikin firgici da tsoro tinda naga hukuncin da aka yankewa Muhseen jikina yayi sanyi na rasa meyake yimun daɗi wlh, amma dai yanzu kana ina nazo na sameka??", shuru tayi tana jiran me zece,dariya yayi sosai sannan yace "haba dan Allah karki bani kunya mana! toh menene zesa jikinki yayi sanyi,mak'udan kud'in da kike nema kinsame su har ma sun ninnika yanda kika nema, kuma batare da kinyi wani aiki me wahala ba dan haka kisaki jikinki hajiya aci gaba da buga harka kawai",dariya sosai itama tayi sannan tace "tohm shikenan Alhaji Sulaiman yanzu kana ina nazo nasameka?","Shigowata kenan gida, dan na gaji zan d'an watsa ruwa around 5:00pm kisameni a guest house d'ina", cewar Alhaji Sulaiman"ok tohm shikenan in Sha Allah zanzo", tana gama fad'ar hakan ta yanke wayar tare da ajiyeta ta mik'e ta shiga bedroom d'inta tana ta zabga murmushi,bayan wasu mintuna da basu gaza arba'in ba ta fito, fridge ta bud'e ta ciro madarar hollandia me sanyin gaske zubawa tayi a cikin glass cup ta koma saman sofa ta zauna tare da kwalawa me aikinta kira Jumma dake kitchen tana mopping tajiyo kiran, da sauri ta ajiye mopper d'in ta fito tana fad'in "ranki yadad'e gani"yawwa Jummai dan Allah kid'an sama mun abu me sauk'i wanda zanci dan yunwa nakeji tafad'a tare da kai kallonta wurin da wayarta take a ajiye saboda ganin takawo haske"toh ranki yadad'e, Jummai tafad'a tare da juyawa zata fita"mik'omun wayata tajiyo muryar uwar d'akin nata tafad'adawowa tayi ta d'auki wayar ta mik'a mata sannan tafita5 miscall tagani na Umman su Muhseen seda gabanta yafad'i amma tadake tare da bin kiranlokacin da kiran yashiga Zainab ce ta shirin d'agawa amma Ummu ta dakatar da ita tare da cewa "bani nayi mata maganaba musu Zainab ta mik'a mata wayarPicking tayi tare da sallama d'auke a bakinta""Wa, alaikis Salam Aunty Laura ta fad'a tare da ajiye cup of hollandia dake hannunta sannan taci gaba da cewa""barka da wannan lokaci Aunty dafatan mun wuni lafiyaUmmun Muhseen bata saurari gaisuwar Aunty Laura ba taceLaura yanzu kin kyauta kenan???? Muhseen fa akaina sharri aka kamashi da lefin da be aikata ba aka yanke masa hukunci na zalinci amma ko sau d'aya bakizo gidan nan ba Laura!!! se mijinki shi dayake ma ba d'an uwana ba shine keta zarya yazo nan gidan yaje court d'in da ake Shari,ar amma Banda ke!!; a tunanina ma ai kece gaba gaba a wannan lamarin amma se naga kin nad'e hannunki shuru Aunty Laura tayi tana sauraron yayarta ta bata katseta ba har se da takai aya sannan tace""Kiyi hak'uri Aunty wlh dama yau nace zanzo wasu uzurirrika ne suka hanani zuwa amma in sha Allah yau zanzo mamaki ne yakamaUmman Muhseen jin abinda k'anwar tata tace, kenan har akwai uzurin dayafi tazo taji yaya halin da ake ciki??""jinjina kai Ummu tayi sannan tace ""gaskiya nayi mamaki Laura dama akwai uzurin dakike dashi dayafi wannan?? Muhseen fa d'anki ne ke kika raineshi ya girma tare dake yashak'u dake amma yanzu dan jarabtar ubangiji tabiyo ta kansa shine har zaki bud'a baki kicemun wai uziri ne ya hanaki zuwa! tak'arasa maganar tare dayin shuru taji me Laura zatace""Kiyi hak'uri Aunty Ummu in sha Allah yau d'in nan zanzo,kamar yanda nafad'a miki abubuwa ne sukaimun yawa wallahi, amma tinda nace zanzo ai magana ta wuce ko??ta k'arasa maganar tare da jefa mata tambaya"""Hmmmm Laura kenan shikenan Allah yakawoki Ummu tana gama fad'ar hakan takashe wayar tana duban Zainab data cika famm tamkar zata fashe dan takaici, Aunty Laura tabata mamaki wlh Kuma ba k'aramun haushinta taji ba""gsky Ummu wlh aunty Laura bata kyauta ba sam,ko batazo dan kowa ba ai zatazo dan Yaya Muhseen""toh Zainab yazanyi da ita kinajin dai abunda tafad'a sedai kawai mu kyaleta kowa yagyara yasani haka ma kowa ya 'bata yasania 'bangaren Laura kuwa jin Ummu ta yanke wayar yasata ta'be baki tare da cewa ""bani nakar zoman ba rataya aka bani, matsalarki ce batawa ba Muhseen d'in banza, kud'i nafiso fiye dashihaka taita banbamin fad'anta ita kad'ai✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
0 Comments