🌹 *RASHIN TABBAS* 🌹Story & writing ByMaryam Naseer Ibraheem (jagabar royal star)wannan labarin k'irk'irarre ne,Kuma nayishi ne domin fad'akarwa da kuma ilimantarwa ban yishi Dan cin zarafin kowa ba idan yayi dai dai da halin wani toh ayimun afuwa🙏🙏*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A}https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu*BISMILLAHIR RAHMANUR RAHIMPage 5 & 6___________Da k'arfi Muhseen ya runtse idanunsa jin zafafan kalaman da d'an sandan nan ke jifansa dasu.Hawaye ne zafafa suka shiga wanke masa fuska amma babu tausayi haka d'an sandan nan ya dinga bal-bale shi da masifa seda wani daga cikin "yan sandan yayi masa magana sannan yaja bakinsa yayi shuru da alama shine babban su a wurin.k'arasowa yayi gaban Muhseen ya dafa kafad'arsa cikin tausayawa yace"ka kwantar da hankalinka indai baka da hak'k'i se Allah ya saka maka,domin Allah baya zalince,kuma ya sanyashi a tsakanin mu abun haramtawa dan haka duk wanda yayi zalinci Allah baze barshi ba,kacire damuwa a ranka ka dage da addu,a in sha Allah sekaga k'arshen zalincin da akai makajinjina kai Muhseen yayi tare dasa hannu yagoge hawayen dake zubo masa yace"nagode sosai kuma in sha Allah zanyi amfani da shawarar ka dakyau d'an sandan yafad'a tare da bubbuga kafad'ar Muhseen sannan yawuce wajan wani gandiro ba magana yayi masa akan abawa Muhseen kaya irin na kowa dake gidan prison d'inbayan an bashi kayan ya saka aka zo dawani wanzami nan take babu 'bata lokaci aka askewa Muhseen gashin kansa tassannan aka shiga dashi cikin gidan prison d'in domin akaishi 'bangaren wad'anda aka yankewa hukuncin kisa Wannan kenantunda aka tafi da Muhseen Ummu ta zube a wajan tana rusar kuka tamkar ranta ze fita ita da su zainab,Alhaji Sulaiman ne yak'araso wajanta yana jifansu da wani irin murmushi me manufofi daban-dabanyana isowa yayi gyaran murya tare da cewa"toh kunga dai k'arshen munafuki jin kunya,kuma ni ba, a had'a hanya dani a zauna lafiya, kamar yanda nagaya muku gashi ya tabbata cikin zafin rai da k'unar zuciya Ummu ta d'ago jajayen idanunta tazubawa Alhaji Sulaiman su a take yaji gabansa ya yanke ya fad'i dan ba k'aramun tsorata yayi da kallon nata babe ankara ba yajiyo dashashshiyar muryar ta tana cewa"Ubangiji baya bacci, kuma baya zalinci shine yasan zahirin lamarin nan da bad'inin sa,daga yau zan dik'ufa baji ba gani inta kaiwa Allah kukana akan wannan zalinci da kukai mana kaje kayi sauraro.ta k'arasa magana da kwarin gwaiwa tare da share hawayen idanunta ta mik'e tsaye tare da kallon su zainab"kudena kuka kutashi muje gida muna da Ubangiji dan haka muje mukai masa kukan muMik'ewa sukai jiki a mace suka shiga motar su k'irar vibe sannan zainab taja suka tafiAlhaji Sulaiman kuwa mutuwar tsaye yayi a k'asan ranshi yake cewa""matar nan da alama fa itama zata kawomun matsala, dole naduba lamarinta idan har naga da matsala se nayi maganintayana cikin wannan tunani Brr Mahraz yanufoshi yana ta sakin murmushi yana isowa gaban Alhaji Sulaiman yatsaya tare da cewaAlhajin Allah yau dai burinka ya cika ka wulak'anta rayuwar Muhseen yak'arasa maganar yana wata shegiyar dariya ta muguntashima dariya yayi sannan yaceshima dariya yasaki sannan yak'ara da cewa ";kwarai kuwa amma duk da haka da saura aiki be k'are ba wannan tsohuwar naga alamar zatai taurin kai itama se nayi maganin ta(yana nufin ummun su muhseen) ta'be baki Brr Mahraz yayi sannan yace"wannan ai me sauk'i ne tinda kagama da Muhseen ai kayi me wahalar yanzu, ya maganar sauran kud'ad'en aikina kasan? yayi masa tambayar yana kallonsakarka damu barrister kajira kawai zakaji alert very soon yak'rasa maganar yana bin gefen Brr Mahraz yawucebaki a sake Brr Mahraz yake binsa da kallo domin ba haka sukai dashi ba, alk'awari sukai a ranar da aka gama Shari,ar suna fitowa ze cake masa kud'in sa cash, amma shine tinkafin aje ko Ina ze yimasa haka kallon Alhaji Sulaiman yayi lokacin har yaje jikin motarsa ze Shiga d'aga murya Brr Mahraz yayi yanda Alhaji Sulaiman zejishi sosai yacewlh! Wlh! Idan har banji alert d'in kud'ina ba daga yau zuwa gobe sena tona maka asiri, alkawari ba necak Alhaji Sulaiman yatsaya jin kalaman Brr Mahraz juyowa yayi yakai dubansa gareshi fuskarsa k'unshe da murmushi yace"Allah ko!?, idan nace bazan cika kud'in ba kenan hakan na nufin zaka iya ja dani??Shima Brr Mahraz murmushi yayi dan shima mugun kansa ne sannan yafara takowa zuwa gaban Alhaji Sulaiman yace"Yes zan iya ja dakai bama kai ba har wad'anda kake ganin sune gatan ka kuma nagaya maka nakuma mai maita maka muffin banji alert d'in kud'ina ba toh komai ze iya faruwakasani bakai kad'ai ka iya shu.umanci ba, bakai kad'ai ka iya mugunta ba, Kamar yanda kakejin Kai ka isa ka kai ni fiye da hakan nakejin kaina, dan haka mu zuba ni dakaiyana gama fad'ar haka yajuya yawuce wajan motarsa ko waiwayen Alhaji Sulaiman be kuma yi bashima Alaji Sulaiman tashi motar yashiga yajata a fusace yabar wajan******************Tinda suka dawo gida sukai jigum-jigum tamkar anyi musu mutuwa, idanuwan su duk sun bushe hawayen ma yadena zubowa sedai rad'ad'in dake cin zuciyarsu"Ummu ni Ina ganin mu d'aukaka k'ara ko Allah zesa a dace musami adalci cewar zaynab girgiza Kai Ummu tayi sannan tace"Zaynab kotun ubangiji ita yafi can-canta mukai k'ara inda ba,a zalinci idan har Muhseen bashi da hak'k'i wlh se Allah yafitar dashi"haka ne Allah ubangiji yatonawa duk me hannu a ciki asiri,kuma in sha allah Allah bazasu gama da duniya lafiya ba aisha tafad'a tana sharar hawaye Allah sarki✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️Mrs A ceJagabar royal star💪💪
0 Comments