🌹 *RASHIN TABBAS*🌹Na Maryam Naseer Ibraheem (jagabar royal star)*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A}*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu*******-----------------*******Labari Mai cike da*Rashin imani*Rashin adalci*Zallar cin Amana*Makirci da yaudara*Sharri da k'azafiWannan labarine me jijjiga zuciyar duk wani me imani,akwai abun tausayi kudai ku K'ara gyara zama domin jin yanda zata KayaBISMILLAHIR RAHMANUR RAHIMPage 3 & 4__________________Jinjina kai alk'ali yayi sannan brr Mahraz ya koma ya zauna yana Kai dubansa in da Alhaji sulaiman yake a hakimcewani shu,umin murmushi suka sakarwa juna lokaci guda"Yan rubuce-rubuce Alk'alin yayi sannan ya d'ago yana k'ara gyara zaman glass d'in fuskarsa yacesakamakon tarin hujjoji da kowane 'bangare suka zo dashi da kuma shedu a kan kisan wannan baiwar allah Raudah wadda bata jiba bata gani ba wannan kotu me adalci ta yankewa wanda a ke tuhuma wato MUHSEEN IMAM ALI hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da horo me tsanani na tsohon shekara shida yana gama fad'in haka yabuga "yar gudumar dake gefensa mutanen dake zazzaune suka mik'e tare da cewa kotuuuufad'ar irin tashin hankalin da ummun su Sulaiman ta ke ciki 'bata bakine,wane irin kuka take tamkar ranta ze fita gaba d'aya tafita hayyacinta sisters d'in Muhseen ma zainab da Aisha kuka suke tamkar zasu shid'edangin ummun su muhseen kowa kagani kuka yake babu ji babu gani abun tausayiMuhseen kuwa mutuwar tsaye yayi gaba d'aya komai nashi yatsaya cak,tashin hankali kenan wanda ba,a sa masa ranaKukama guri yake samu,domin kuwa muhseen yakasa kuka amma idanuwan nan nashi jawur tamkar garwashin wuta baya fahimtar meke faruwa kwata kwatawani d'an sanda ne yazo ya kama tankad'a muhseen Cikin fitar hayyaci muhseen yafara tafiya tangal tangal tamkar ze kife,kallo d'aya zakai masa ka tabbatar baya cikin nutsuwarsa,gaba d'aya ya susuce ya birkice d'an sandan nan kuwa haka yaketa tisa keyarsa domin a tafi dashi gidan yarina gigice zainab ta d'ago tana fad'in "Ummu zasu tafi da yaya muhseen shikenan zasuje su kashe mana shi munshiga uku wayyoo Allah ummua razane ummun muhseen ta mik'e tabiyo bayansu suma su Aysha biyosu sukayi suna kuka wiwiseda akaje bakin motar sannan suka tsaya da muhseen,da gudu suka baibaye muhseen suka rungume shi wani irin kuka suke natashin hankali Se a lokacin muhseen yaji wani irin kuka yazo masa,aikuwa a take ya kece da wani irin kuka naban mamaki tamkar k'aramun yaro had'asu yayi gaba d'ayansu ya rungume su a jikinsa yana kuka hawayensa na zuba a jikinsu,suma kukan suke tamkar bazasu dena bacikin kuka ummun su tafara cewa"nasan bakai ka aikata kinsan nan ba muhseen wlh nasan bazaka iya kashe Koda sauro ba bare wadda kaso so mara misali,akwai makirci a cikin lamarin nan da munafurci shiryawa kawai akayi saboda a tozarta muko sun kasheka ruhinka baze tafi a banza ba,alhakin ka baze barsu suyi rayuwa cikin salama ba,wlh se sun wulak'anta Kuka ne yaci k'arfinta ta kife kanta a k'irjin muhseen tana kuka me tsuma zuciya gwanin tausayiShima cikin k'arfin hali yafara magana a raunane"Kiyi hak'uri ummu na,ki gafarceni,bani da kalaman da zan rarrashe ki dasu ke da k'annena,amma inaso kisani BANI NAKASHE RAUDAH BA hasalima bansan waye yakirani a waye ba a daren da aka kashetazanyita addu,a Allah ya bayyana gaskiya kiyi hak'uri ummu na zanyi kewarku,ku yafemunyak'arasa maganar yana k'ara sakin wani marayan kuka gyaran murya d'an sandan dake bayansu yayi sannan yace"hajiya ba jiranku zamu zauna yi ba,ku sashi a mota mutafiyafad'a yana kallon gandirobobin gidan yarinKamashi sukai suka fara turashi kamar tsohuwar mota suka bud'e mota suka sakashi a cikicarko carko ummun su muhseen tayi ita dasu zainab da sauran "yan uwa anata koke-koke tamkar gidan mutuwaMuhseen kuwa tinda ya shiga motar gidan yarin ya juyo da kansa ta wajen raga ragar jikin motar ya k'urawa mahaifiyarsa ido tare da sisiers d'inshi da family d'insa da suketa shar'bar kuka,da haka har motarsu tatashi tasoma tafiyahannu suka shiga d'aga masa suna k'ara narkewa da kuka har motar ta 'bacewa ganin su Allah sarki *Prison*Cigaba da ihu ragowar mutanan d'akin sukayi,ba'ba da goje kuwa se tikar kokawa suke tamkar a gidan dambeWani gandiroba ne yaji hayaniyar tayi yawa ya nufo d'akin da sauri dan yaga meke faruwayana zuwa yaga anata dambe tamkar k'ana nan yara mamaki ne yakamashi duk da ba yau suka fara bata shidai al,amarin su mamaki yake bashiTsawa yadaka musu tare da cewa"dallah ku saurarawa mutane,ku mai yasa Kamar dabbobi haka kuke baku da lissafi,yaushe zaman wajan nan ze zama darasi agare ku ne?Shuru sukayi suna sauraronsa,dayawansu se kumbura baki suke kamar zasu fashe gashi ba damar mayar da martaniKallon goje da ba'ba yayi wad'anda har yanzu basu dena haki ba saboda damben da Suka Sha yace"Ku kuma ku taso, tinda Baku da mutunci yau se na azabtar daku da ayyuka masu wahala ya k'arasa maganarsa tare da bud'e musu k'ofarda gudun gaske motar tashigo harabar gidan yarin,bayan tayi parking aka bud'ewa su muhseen k'ofa amma ko k'wak'k'waran motsi yakasayi hasalima sama- sama yakejin me gandiroban ke fad'aseda gandiroban yasa hannu ya jawoshi waje sannan ya motsa a hankali yad'aga manyan idanunsa wad'anda suka koma tamkar an watsa barkono saboda tsananin tashin hankali,gashi duk sun k'ank'ance sun kumbura sunyi luhu-luhuWurin yakebi da kallo zuciyarsa na masa ciwo tamkar zata bugaGanin al,amarin yake tamkar a mafarki,Wai yau shi ake tuhuma da lefin kisa! kisan ma me muni kisa na rashin imani,kuma wadda yafi k'auna a rayuwarsa ita ake tuhumarsa daya kasheta"Innalillahi wa inna ilaihirraj un ya furta a hankali sannan yafara tafiya yana bin bayan gandiroban kamar yanda ya umarce shi"Yar k'aramar k'ofa aka bud'e musu wadda seka durk'usa zaka shigaDuk'awa yayi yashiga tare da ambaton sunan Allahwani gandiro ba ne ya umarce shi daya cire takalmansa cirewa yayi jiki a sanyaya,sannan suka fara cajeshi babu komai a jikinsa se wani zoban azurfa dake yatsansa na tsakiyad'an sandan ne yakai hannu ze zare zoband'agowa muhseen yayi yakai dubansa kan d'an sandan nan cikin dashashshiyar muryarsa yace"Dan Allah karka rabani da zoban nan,rRaudah ce tabani shi ita tasamun shi da hannunta karka rabani dashikallonsa d'an sandan yayi sannan yace"ai bakasan darajarta ba,kuma baka rik'e alk'awari ba da kasan darajarta da Kuma kana da imani da baka rabata da rayuwarta ba,amma saboda baka da imani zuciyarka ta bushe haka ka hallakata har lahira ya k'arasa maganar tare da fisge zoban daga yatsan muhseen......✍️✍️✍️✍️✍️✍️Idan kinaso kisani farin ciki toh sharing kawai nake buk'ataJagabar royal star ce💪
0 Comments