🌹 *RASHIN TABBAS*🌹 P 1-2Story & writer by Maryam Naseer Ibraheem (jagabar royal star) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu* Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ALLAH mad'aukakin sarki me yanda yaso,a sanda yaso,a inda yaso.ALLAH ka k'ara tsira da aminci ga manzan rahma s.a.w, ALLAH kaimana jagora Dan sirrin la,ilaha illallahu muhammadur rasulullahi s.a.w,ALLAH kashiga cikin lamarin mu yanda muke Shirin farawa lafiya ALLAH kasa mugama lafiya Dan tsarkin ruhin manzan ALLAH s.a.w,ALLAH ka dafa Mana ameeeen ya rahman ya raheem🤲🙏Sadaukarwa:-Na sadaukar da wannan littafin me suna "RASHIN TABBAS" ga kafatanin "Yan k'ungiyar *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* ALLAH yak'ara Mana dankon zununchi,da d'aukaka,ALLAH yak'ara had'a kan mu,ALLAH yak'ara Mana k'arfin gwaiwa, ubangiji yabamu ikon rubuta alkhaeri Koda yaushe.BISMILLAHIR RAHMANUR RAHEEM____________________'Dakin cike yake taf da samari yawancin su matasa ne,duk da kasancewar d'akin k'arami amma haka aka cunkusa su a cikinsaakwai wad'anda suka manyanta sosai a cikin d'akin amma fa manyan banza,dan dayawansu abunda sukeyi na rashin kamun kai yayi yawa tamkar ba dattijai bakowa harkar gabansa yake masu wasan banza sunayi masu musu sunayi,wasu kuma abun duniya duk ya ishe su sun zauna jigum jigumWani k'aton mutum ne yayi gyaran murya tare da cewa "guys yayaneeeee wai mu haka zamiyita zama ne a cikin wannan gidan yarin,kowa a cikin d'akin nan ya tabbatar angama Shari,arsa an yanke masa hukuncin kisa toh me muke jira ai yakamata muyi tunanin hanyar da zamu samarwa kan mu mafita ko yak'arasa maganar tashi Yana binsu da kallo d'aya bayan d'aya yana jiran yaji me zasu ceShuru kowa yayi ana kallon kallo tsohon mintuna goma kowa yakasa magana domin su kansu sunsan cewa abunda yake nufi shine su gudu,Kuma guduwa daga cikin wannan gidan yarin ai babban hatsari nekallonsu yakuma yi rai a 'bace yace "aikin banza aikin wofi kunyi zuru zuru kuna kallona tamkar wasu mutanan arzik'i,kaf cikin d'akin nan waye me imani??gaba d'ayan mu babu me imani,tinda duk rashin imani muka aikata aka kawomu nanakwai masu kisan kai,akwai mugayen "yan fashi da makami,akwai shahararrun "yan kidnapping akwai shahararrun 'barayi da masu fyad'e wane irin rashin imani ne babu me aikatashi a cikin d'akin nanamma saboda ku gidadawa ne hanyar da zamu gudu daka wannan gidan yarin ne kuke tunanin tayi muku wahala banzaye wawaye kunyi asara wlhyak'arasa maganar yana jan wani dogon tsaki Wanda hakan ya fusata wani a cikin d'akin Dan haka cikin fushi yafara magana da muryarsa irin ta rik'ak'k'un "yan daba"dallah malam gafara can ajawo,kaja dakai kazo kana mana wata maganar banza har kana nema ka zage mu,kai ma ai kayi asarar ba mu kad'ai mukai ba,kai meyasa bazaka kawo shawarar yanda zamu gudun ba saboda kaima kasan kanka na kifi ne baka da basira shiyasa kake neman shawarar mu,dan haka mu se munyi tunani munga abunda yadace tukunna Hayaniya ce tafara tashi a cikin d'akin kowa na fad'in albarkaci bakinsa wasu na cewa abunda goje yafad'a gsky ne wasu Kuma suna goyan bayan ba'ba wanda yagama magana yanzu,dan dayawansu sunji haushin zagin da goje yayi musuhaniya sosai sukeyi goje kuwa ransa in yayi dubu toh ya 'baci dan haka cikin hassala yamik'e tare da buga k'afarsa a k'asa yajata baya tare da dunk'ule duka hannayensa yana kallon ba'ba yace"Kai d'an akuya haihuwar asara ni zaka kalla kace mun me kan kifi shekarata 20 ina fashi da makami ba,a ta'ba kamani ba se wannan karan da akaimun talala har akaci nasara akaina,idan ka Kai shege kazo mu buga mu fidda raini yauTini ba'ba ma yamik'e duk da kasancewarsa siriri gakuma shaye shaye duk yakuma sa shi yafita daga hayyacin sa dan goje yafi ba'ba k'iba sosaihannunsa shima ya dunk'ule Yana kallon goje Yana cewa"Shege ka fasa ni dakai,ragowar mutanan d'akin kuwa tini suka mimmik'e tsaye suna k'ara bud'a musu fili wasu suna cewa "goje! goje!! goje!!! suna d'aga hannuwasu Kuma ba'ba sukeyiwa kirari suna k'ara hassala shiabun haushi abun takaici har dattijan da suke d'akin an rasa me dakatar dasu daga wannan kokawar da suke shirin yigoje ne yatafi da gudu yakaiwa ba'ba wani naushi a gefen k'irjinsa cikin azama ba'ba ya kauce goje yadaki iska kafin ya juyo ba'ba yasa k'afarsa yadaki bayan goje da iyakacin k'arfinsa aikuwa a take goje yafad'i a kasan d'akin ruff da ciki ihu gaba d'aya d'akin ya d'auka manyan da matasan suka fara tafawa ba'ba yayin da wasu suka shiga 'ba'b'bakawa goje dariya Kamar ba gobewani tsoho ne da a k'alla zeyi shekara 50 ya tsagaita da dariyarsa yace"Kaiiii jama,a anayi munajin dad'i dama an kwana biyu ba,a bawa hammata iska a cikin d'akin nan ba,a caskale yanda yakamata mazajena motsa manayak'arasa maganar yana ci gaba da dariya yana kallon goje wanda har yanzu be d'ago ba saboda takaicia fusace goje yataso jin abunda tsohon nan yafad'a beyi wata wata ba ya cakumo ba'ba nan fa kokawa ta 'balle a tsakanin su cigaba da ihu sukayi mutanan d'akin suna k'ara bud'a musu filiDuk wannan abun dake faruwa gandirobobin gidan yarin basu san meke faruwa ba dan lokacin rana ce sosai,wasu suna harabar gidan yarin suna zaune sunata hira,wasu kuma sun kwashi wasu daga cikin "Yan gidan yarin sunje kotu dasu domin gudanar da shari,ahKokawa sosai su goje keyi anrasa Kuma me rabasu se zagin juna suke suna aibata junan su shi da ba'ba *Court*an gudanar da shari,ah daban-daban kafin azo kan Shari,ar muhseengaba d'ayan jama,a kowa jira yake yaga yaya wannan Shari,ah zata kasance domin case ne me matuk'ar rikitarwa Shigowa akai da muhseen cikin court d'in hannunsa sanye da ankwa yarame ya lalace gaba d'aya yafita daga kamannin sa kansa a k'asa dan kwata kwata bayaso ma yad'ago yakalli mahaifiyarsa da "yan uwansa a wannan yanayininda ake tsayawa aka umarce shi dayaje ya tsaya,shiga yayi wurin ya tsaya a zuciyarsa kuwa tini yagama yanke shawara kuma hakan ze aiwatar domin yasamawa kansa salamatinda aka shigo da muhseen mahaifiyarsa taketa faman sharar hawaye tare da duk ahlinsa masu k'aunarsa dan duk wanda yasan muhseen kuma yaganshi a wannan halin toh tabbas seya tausaya masaanfara gudanar da shari,ar su muhseen d'in nan take lauyan Wanda yake k'ara yadinga kawo hujjoji bayanannu akan tabbas muhseen shine yabi raudah har gidan aurenta yasa mugayen makamai ya daddatsa sassan jikinta har ma yacire wasu abubuwa daga jikintawanda kafin yayi hakan an tabbatar da cewa ya furta mata muddin ta auri wani ba shi ba toh shine zeyi ajalinta ita dashi gaba d'aya ze had'a yakashe su Duk wasu hojjoji lauyan me k'ara yagabatar dasu, inda alkali ya juyo da tambayarsa kan muhseennan take muhseen ya jinjina kansa alamar tabbas duk ya aikata hakandubansa alkalin yayi dakyau sannan yace "ka tabbatar Kaine ka aikata wannan kisan ka n na rashin imani ko???"Nine na aikata ya mai girma me Shari,ah cewar muhseen ya k'arasa maganar yana kallon k'asa sam yak'i d'agowa bare yakalli mahaifiyarsa da sauran "Yan uwansagyaran murya alk'ali yayi sannan yace"Lauyan wanda ake tuhuma kana da magana?cikin mutuwar jiki da rauni barr kamal yace"bani da magana my Lord,sedai ina rok'on wannam kotu me adalci data sassautawa muhseen hukunci nagode yafad'a tare da komawa ya zaunabrr mahraz ne yamik'e tare da cewaya mai girma me shari,a yakamata kotu tayiwa muhseen hukunci dai dai da abunda ya aikata domin yazama darasi ga "yan baya da masu mugun hali irin nashi......✍️✍️✍️✍️✍️✍️zanyi amfani da wannan damar wajan bawa "Yan editing room d'in mu hkr sakamakon dad'ewa danayi banyi typing ba,matsaloli ne Suka jawo hakan Amma ynxu alhmdllh komai yayi dai dai se gdyr allahMore comment more typing✍️✍️✍️✍️Plz sharing🙏
0 Comments