💞💕 *SO KENAN* 💞 💕 9-10JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI NAKHADIJA UMAR ABDULLAHI GARKUWAR JARUMAI CE 💪🏽(A KARANTA DA HAKURI BABU EDITING😂)بسم الله الرحمن الرحيم Dukan khadija ake yi ta ko ina har sai da ta dena motsi sannan yayan ta ya barta yana huci ya fice daga gidan, itama umma ranta a bace yake .Suhail kuwa kwanciya yayi yana ta juyi a dakin sa hannun sa dafe da marar sa haka.inna ta zo ta same shi hankalin ta a tashe take masa magana Amma shru babu amsa da gudu ta fita waje ta kira abokan jona suka shigo suka dauke shi sai asbti da yake asbtn gwamnati ne haka aka yasar da jona a kasa har saida yaa galabaita sosai inna ta fara masifa sannan suka karbe shi anyi saa babban likita yazo kuma Yana da kirki sosai ya shiga checking dn lafiyar jona inna da abokan sa suna waje sunyi jugum jugum wani daga cikin abokan jona dn ne wanda wiwi bata gama sakin sa ba y dubi inna cikin magnar yan shaye shaye yace "" caucau hajiya innar mu kawai mu afka muga abnda wannan dan laawan yake wa jona banza inna tayi dashi ragowar suka mike zasu shige rai a bace inna ta mike ta fara masifa zuciyar ta na mata daci tace """ ai gara ku shiga ku karasa shi yarona mai mutunci kuka bata mn shi da shaye shaye gashi nan Allah kadai yasan me ya faru dashi ku kuna da gata shi kuma Suhailu ni kadai gare shi ni din ba wata bace bare na taimaki rayuwar sa dn Allah ku fita daga rayuwar Suhailu dn Allah kubar mn shi y dawo Suhailu na wa dana sani a da tana kaiwa nan ta fashe da kuka tana hade hannyen ta alamr roko.Hankalin kowa yayo kansu wasu na tausaya mata wasu na kallon ita ce bata bashi tarbiyya ba.Daidai nan wata nurse ta fito ta kira inna da sauri inna ta mike ta shiga dakin da aka nuna mataa bakin ta dauke da sallama ta shiga wajan zama likitan ya nuna mata sannan ya dubi inna a nurse yace "" ya kike da mara lafiya ? "" Jika na ne inna tace tana raba idanu hankalin ta ya kasa kwanciya ganin babu Suhailun ta cikin dakin .Gyaran murya likitan yayi yace ciwon marar da jikan ki ya keyi ba wata matsala bace dama tana faruwa fa mace ko namiji Wanda suka balaga shaawa ce wato dai akwai bukatar ayi masa aure saboda zaa iya samn matsata a marar sa sakamom yawan maniyin dake marar tasa ,sannan kuma matsalar ita ce kodojin jikan ki gaba daya sun lalace dalilin shan sigari da ta wuce iyaka bincike ya nuna Yana iya shan sama da kwali biyar a rana sannan yana maida hayakin ta cikin sa sbd haka ana bukatar koda guda daya sannan zaa cire nasa duka a samu a dasa masa wata.Wani irin murdawa cikin inna yayi take kanta y fara juyawa hankalin ta yakai kololuwa wajan tashi idanun ta fal hawaye tace likita ka cire nawa duka ka sawa Suhailu nidai ya rayu kawai"" girgiza kai likitan yayi sannan yace aa baba ana bukatar koda wacce mai ita bai haura shekara hamsin ba kema yanzu tattalin lafiyar ki ake kinga kuwa ba zaa rage miki ba.Kuka sosai inna takeyi tana rokon likita ya cire kodar ta ya saka wa Suhailu ta yayi matukar tausaya mata likitan.A jiyar zuciya ya sauke sannan yace ""ba yanzu ne zaayi aikin ba akwai wani poundation na Sahal Abdallah poundation suna taimaka sosai waja saka kudi a bankin asbt yanzu a ciki zaa bawa jikan ki magani da allurai idan sun kare sai ayi maganar aikin shima kuma kudin aikin zanyi mgna da PA dn Sahal dn sai a taimaka a biya masa amma fa ba kodar ki zaa saka masa ba kudai nema ko a dangi.Hankalin inna ta dan kwanta godiya sosai ta shiga yiwa likitan sosai yasa aka raka ta dakin da aka kwantar da Jona.Kwance yake sambal kamar gawa hannun sa daure da drip lokaci daya yayi wani fayau dashi ya rame dogon hancin sa ya kara ftowa a hankali inna ta karasa ta shafa sleeping face dn sa tace Allah y baka lafiya Suhailu.Wata nurse ta barwa jona ta koma gida domin dakko abubuwan amfani wanda zata zauna dasu a sbtn Wannann kenanBangaren mai martaba Sahal y shiga ya same shi a kishingde yana Jan cazbaha suka gaisa suka dan taba hira kafin Sahal dn y fto perking space ya nufa ya tarar an wanke masa motocin sa dogarai na tsaitsaye suna jira y fto yana isowa suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa suma dai daga musu hannun kawai yake yi ya wuce wa mota daya kawai yake son fita da ita da sauri driver y taho Sahal dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu ya mika masa mukullin yaja motar sa yayi gaba.Direct asbtn sa dake jikin gidan sarautar ya nufa kmr ba shi ba haka ya dinga washe baki yana gaisawa da patient musamman ma yara.Saida yayi sallar laasar sannan ya fto y nufi gida.Wata matashiyar budurwa ce wacce ba zata wuce shekara goma sha takwas ba zaune gaban madubi tana shafa mai a skin dn ta tana gama shafawa da goga yar puwder kadan da kwalli White lips ta saka a labban ta ta mike ta nufi ward robe ta jima ta tsaye tana kallon kayan ciki kafin ta dakko wani bakin less mai adon golden a jiki dnkin riga da skirt ta saka ajikin ta daidai jikin ta haka ya zauna das a kugunta gwanin ban shaawa. Gefen sarkokin ta ta nufa ta dakko wata siririyar sarkar gold da yarin ta ta saka ta saka agogo ta shima gole da zobuna da suka kara kawata fararen yatsun ta wanda akayi wa jan lalle takalmi ta dakko half cover golden da dan siririn mayafi shima gold fadar kyawun da tayi ma bata lokacine Nusaiba kenan ya ga Abdulhamid saraki kanin sarki Abdallah mahaifin Sahal Kuma shine galadma a yanzu .Nusaiba doguwa ce ba sosai ba bata da kiba saidai jikin ta murje yake tana faffadan kugu wanda yasan tsuke daga kasa kirjin ta a cike yake da dukiyar fulani fara ce soll kyakykyawa mai Dara daran idanuwa gashin idon ta zara zara da dogon haci da dan karamin baki wanda zaka zata cokali bazai shiga ciki ba.Nusaiba yarinya ce mai hankali da tarbiyya tana girma ma dk na sama da ita kkda bawa ne tana matukar son Sahal shima Kuma yana son ta sosai saidai jin kai irin na Sahal yasa ita ce ke nuna masa kauna shi kuma yana basarwa amma ko kadan ta wuce lokacin da take kiran sa hankalin sa yana matukar tashi baya samun nutsuwa har sai yaji daddan saurtin abar kaunar sa.Sanyin yamma be ya buso ya farkar da khadija daga suman da tayi ko ina jikin ta ciwo yake mata dakyar ta rarrafa tana hawaye ta shige dakin ta ta kwanta rigingine taba kallon silin zafafan hawaye na kwaranyo wa daga Ramin idanuwan ta .Bata jima da kwanciya ba umma ta shigo da sallama ciki ciki ta sa kafa ta zungure ta tace ''' tashi dan uban ki"" babu wata gardama khadija ta mike zaune tana raba idanu tayi matukar tsorata da yanayin da ta ga ummar dn bata taba ganin ta cikin wannan yanayin ba , tana cikin tunanin ta tsinto muryar umma tana mata tambayar data sa ta kara makalewa a jikin bango,Rai a bace umma ta daka mata tsawa tace ""nace menene ya hadaki da jona har kuka rungume juna a tsakiyar hanya shiru khadija tayi ta kasa cewa komai saida umma ta dakko muciya tayi kan ta da ita,Sanin yanda jikin ta ke mata ciwo yasa khadija ta bude baki cikin kuka tace "" dn Allah umma kiyi hakuri ki fahimce ni wllh shi nake so kara kasa kunne umma tayi tace "" kika ce me? Ina son shi umma khadija ta kara fada kanta a kasa idon ta cike da hawaye sakin muciyar umma tayi ta zauna kasa dabas a kasa tace ""Jona kike so Khadija?......Oum sharifat ce
0 Comments