💕💞SHI NAKE SO💕💞1-2JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI NA KHADIJA UMAR ABDULLAHI GARKUWAR JARUMAI CE 💪🏽بسم الله الرحمن الرحيمKhadija! Khadija!! Khadija!!! wata dattijuwa take ta kwalawa daga tsakar gida , jin shiru yasa ta mike ta shiga wani karamin daki dake kusa da ita , budurwa ce zaune kan katifa ta kurawa wayar dake hannun ta ido ko kiftawa batayi a tsaye matar ta tsaya tare da rike haba tana kallon budurwar dake gaban ta cike da takaici ta kwala mata kira ranta ya kai kololuwa wajan baci.A firgice budurwar ta ta dago ta kalli matar da ke tsaye a kanta cikin in ina ta fara mgna """ um um umma ""kallon banza wacce ta kira da umman tayi mata sannan tace """ wato ke ban isa na fada miki kiji ba ko kullum kika saka waya a gaba bakya jin kowa bakyajin komai ko? To bani wayar umman ta fada tana miko hannu boye wayar khadija tayi a bayan ta idon ta yayi raurau kamar zatayi kuka tace """ dn Allah umma kiyi hakuri wllh na dena.Da matukar mamaki umma take kallon khadija tace "" wai menene a wayar ne da bakya so a gani ? Anya kuwa khadija akwai gaskiya a lamarin ki? Akwai wllh umma ba abnda nakeyi Allah na rantse miki , yanda take ta rantsewa ya kara jefa umma cikin shakku da mamaki cikin ranta tana tnanin dole ya bncika abnda khadija takeyi da wayar ta .Sauke ajiyar zuciya umma tayi tace "" to ki tashi lokacin makaranta ya kusa ""ai kafin umma ta karasa fada khadija tayi saurin mikewa har tana kifawa ta fito tsakar gida ta dauki bokiti ta diba ruwa ta shiga toilet umma da khadija ta bari tsaye ta jiyo tana kallon yanda take sauri abn ya kara daure mata kai, abubuwan da khadija takeyi kwana biyu ya fara bawa umma tsoro cikin zuciyar ta take adduar Allah y tsare mata autar ta daga dukkan sharriA gaggauce khadija ta gama shiryawa cikin uniform wanda karbi jikin ta sosai tayi matukar kyau tana cikin saka hijab akayi sallama kawar ta ce maryama ta biyo mata suka gaisa da umma khadija ta fito suka fita.Suna fta kofar gida Maryama ta dubi khadija cike da damuwa tace """ kawata yau dai sauri.zamuyi kinga mun kusa makara "" wani kallon banza khadija tayi wa maryama tace "" kema kinsan bazan iya ba dole saina ganshi sannan zan iya karatun gara ma.ki bari kawai ganin sa zanyi bazan tsaya ba sai mu wuce .Sanin cewa ba zata hakura ba yasa Maryama ta amsa mata da ""to" suka cigaba da tafiya.Daidai bakin wata katuwar kwata wani karamin shago ne wansa ake saidai kayan provision daga kofar shagon wasu benci ne guda biyu yayin da samari ke zaune kowannen su kaca kaca dashi kamr bai taba ganin ruwan wanka ba hannyen su dauke da sigari suna zuka wasu harda wiwi .Daidai nan khadija taja ta tsaya ganin kmr basu san da ita a wajan ba yasa ta karasa gaban kantin tayi sallama babu wanda ya amsa sai na cikin shagon.Alawa khadija ta siya badon tana bukata ba saidan ganin wanda zuciyar ta take mararin gani ta ganshi saidai da alamun yau yasha da yawa don baya gane komai daidai zata juya tayi tuntube da kafar mutum kafin ta juyo taga Wanda taci karo dashi ya tashi cikin yanayin maye ya zabga mata wasu tagwayen maruka masu zafi.Idaun khadija ya kawo ruwa Amma haka ta shanye ta dago kanta ta kalleshi zuciyar cike da zallar soyayya wacce ta kasa boyuwa a idanun ta .Ganin ta ki matsawa daga wajan ya sashi saurin kai hannu ya finciko ta ta fada kan faffadan kirjin sa a zafafe ya shiga bata kisses ba tare da ya damu da cewa a hanya suke ba. Hamshakiyar mata ce mai ji da i ko da sarauta kishingde kan wata kyakykyawar kilisa daga gefen ta wata dattijuwa ce zauna kan ta a kasa tana mgana cikin ladabi.""" Ranki ya dade fulanin gobir Kece uwar gida a wajan sarki Abdallah kuma kece mai sawa da hanawa a cikin wannan masarautar babu abnda zai gagare ki Allah y taimake ki babu abnda ke tsayawa a gaban ki baki kawar da shi ba nasara a jinin ki take.Wacce aka kira da fulanin gobir ta saki wani tattausan murmushi wanda ya kawata fuskar ta sannan ta kara jin kanta a sama cike da izza ta ce "" Jakadiya shekara ashirin da biyar kenan har yanzu Takawa bai manta da Suhail ba gashi yanzu duk irin abnda akayi wa Sahal baya tasiri akan sa na rasa wane irin yaro ne shi gashi kinsan bashida kunya ina tsoron wannan yaron yafi karfi na nan gaba dn na ranste koda zan rasa komai nawa yanda na raba Suhail da masarautar nan sai na raba Sahal da ita shima sannan na wulakanta munafukar uwar su kuma na dora Abdulmalik akan kujerar sarautar kinga ni ce zan dnga mulkar Kano gaba dayan ta wannan shine fata na kuma wallahi sai na cika buri na.....Oum sharifat ce
0 Comments