💢💢💢``` DUHUN JAHILCI ```💢💢💢
```labari da tsarawa```
```MAMASHU```
```DA```
```OUM SHARIFA```
```( 2EFFECT EMPIRE)```
``` wannan labari yana kunshe da abubuwan ban mamaki Wanda hankali ko tunani ba zai dauka ba, ko cikin jahilai ba kowa zai aikata irin wannan abun ba, kai ko da cikin dabbobi wasu suna kishin a kusanci matansu, bare mutum mai hankali Wanda allah ya sanya masa zuciya da tunani.```
``` JARUMAI WRITERS WANNAN ITACE KUNGIYAR MU TAKE MU SHINE AL'KALAMI YA FI TAKOBI```💪🏾💪🏾💪🏾
``` Bismillahir rahmanir rahim ```
``` PAGE 2```
........✍✍✍Bai karasa fadar sunan ba fuskar zainab ta dawo masa a zahirin ta,
sai sannan ya fuskanci kuskuren da yake shirin aikatawa, duburburcewa yayi ya fara kame kame zuciyar sa fall kwadayin kara yin tozali da kyakykyawan jikin Khadija wanda yake rikirkita shi,
kallon sa zainab take yi da mamakin yanayin da ta gani a tattare da mijin nata Wanda bata saba gani ba,
Gyara zaman ta zainab tayi ta dora hannyen ta akan table dn ta kalli haydar cike da damuwa tace "" my lafiya kuwa? kodai wani abu yana damun ka "" yamutsa fuska haydar yayi yace "" no I'm okay""
jikin zainab ne yayi sanyi damuwa ta bayyana sosai a fuskar ta kamar zatayi kuka tace "" please my tell me what's wrong ? Dan guntun murmushi haydar yayi tare da cewa "" bakomai sweetheart gajiya ce kawai "" sai yanzu hankalin zainab ya kwanta ta taso daga kujerar da take zaune ta dawo kusa da haydar ta sakalo hannun ta dafa bayan sa ta fara debo abinci a spoon tana kaiwa bakin sa,
dan kadan yaci yace ya koshi, gaba daya abncin bai masa dadi ba, badon zainab bata iya ba saidan baya jin dadin komai nata, hankalin sa yana ga khadija wacce komai nata yake burge shi.
halittar ta, tafiyar ta, maganar ta da kuma abincin ta komai me dadi ne a wajan sa idan ya rufe idon sa ita yake gani tana yi masa murmushi da kuma shagwaba cikin muryar ta mai kama da ana busa sarewa.
yayi nisa acikin tinani zainab tana ta magana amma hankalin sa baya kanta sai da ta sa hannu ta shafa fuskar sa tare dan jan gemun sa kadan sannan ya dawo hayyacin sa tare da yin murmushin yake,
Zainab ta mike tsaye ta rike hannun haydar ya tashi tsaye ta saka hannun ta ta kamo kugun sa ta hada da jikin ta dadda da kuma sassanyan kamshin ta ya doki hancin haydar, amma maimakon yaji dadi sai ji yayi kamar ya shake zainab, a ransa Yana jin dama khadija ce tayi masa wannan rukon,ba zainab ba domin komi na khadija daban ne. " Uhmmmmm ! Ya furta a hankali.
Zainab ta dago ta kalle shi amma bata ce komai ba a zaton ta gajiyar ce,
har bed room ta kaishi ta cire masa jallabiyyar dake jikin sa ta sauya masa zuwa wasu lallausan kayan bacci milk colour.
Kwantar dashi tayi sanna ta sunkuyo daidai saman labban sa ta bashi kiss tace "" doctor na bari naje na gyara wajan na dan watsa ruwa sai na dawo mu kwanta ta karasa maganar tana kashe masa idon daya.
Khadija ya gani ta kashe masa idon ta juya, take ya fara ganin cikakkun mazaunan ta suna juyawa cikin skirt daya kama jikin ta sosai,
baisan lokacin daya tashi zaune ba saidai yana tashi yaga zainab ce, a hankali ya koma ya kwanta ya rintse ido yana tinanin yanda zeyi ya mallaki khadija koda na one time ne, lashe labbansa ya yi tare da gyara kwanciyar sa zuciyarsa ce ta cigaba da harbawa da sauri da sauri ga wata irin shaawa da taka ma shi Wanda bai taba samun kansa a ciki ba.
Dafe kansa ya yi tare da bude idonsa Wanda suka kada sukai ja hade da kankancewa zuba ma kofar toilet ido ya yi lokacin da zainab ta fito daure da towel a jikinta tana goge kanta da karamin towel. Kallon ta ya shiga yi kamar yau ya fara ganin ta tinda ga kan yatsan kafarta ya dinga kalla har zuwa fuskarta tabbas zainab bata da makusa ko kadan amma meysa zuciyar sa ta kwadaitu da khadeeja?.
A hankali ya sauke idonsa tare da rufesu ruf kamar mai bacci, Zainab tagama shirin ta tare da fesa turara masu kamshi da sanyi ta nufi Kan bed din, a hankali ta shafi fuskarsa tace" My ko kayi baccin ne?" Dan motsawa ya yi tare da juyo da kansa ya zuba Mata ido, a dan tsorace ta Mike tace " My meyasa meka ne plz"? Murmushin gefen baki ya yi yace" Bakomi illa cike nake da kishirwa hade da kwadayin samun wani abu". Ya fada yana kara lumshe idonsa.
Murmushi zainab tayi jin kalaman Hydar a zaton ta ita yake bukata, shige masa tayi tare da kashe fitilan bed side ta shiga nuna masa kalolin kaunar da ta tanadar masa, luff ya yi alamar abun bai masa yadda yake so ba, zainab iya kokarin ta yi wajen ganin Hyadr ya saki jiki amma furrr ya ki sakin jikin dole ta hakura ta maida kayanta tare da kwanciya gefensa.
Shima juya yayi ya kwanta amma bacci ya gagari idonsa siffar khadijah ke ta masa ya yawo a kwakwalwarsa.
Shaidan ne ya kuma birkita masa tunani hade da bijoro masa da wata shaawar da sauri ya tashi ya fara laluban zainab Wanda har baccin ta ya fara yin nisa.
Sarrafata ya shiga yi cikin wani bakon yanayi domin khadija ce yake gani ba zainab ba, Sanbatu ya shigayi cikin tsananin shauki yana magana " Ina sonki idona ya rufe ban ganin wata halitta sai ke ki ban dama na mallaki dukkan jikin ki da zuciyarki ina sonki ki sakar min dukka wata ragamar jikin ki". Zainab ta shiga rudu Shin da Ita Hydr ko da wata yake?"
Da karfi zainab ta saki wani numfashi dan ganin hydr yana hayyacinsa kome?"hayyacinsa ne ya dawo jikinsa lokacin da yake kokarin shigar zainab. Saurin tureta gefe ya yi tare da dafe kansa.
Cikin mamaki zainab ta tashi daga kwanciyar da take ta , tace " Wai My lafiya kake kuwa? Ni fa na kasa gane kanka tin da ka dawo aiki". Cikin raunin murya tayi maganar.
Mtseeeeeeeeeeeeeewwwww! Ya ja wani dogon tsaki tare da mikewa ya shige toilet, galalala Zainab ta saki baki cikin alajabi " Me ya ke shirin faruwa dani ne ? Ta tambayi kanta.
A toilet Hydar sakar ma kansa ruwa ya yi yana mai jin radadi a zuciyarsa take kishi ya bayyana karara a fuskar sa " Yanzu haka Deeni yana chan tare da khadija a kan gado"? Yanzu haka suna chan suna soyayyarsu?" Wani irin duhu ne ya ziyarci idonsa tare da kaima bango duka ya furzar da wani irin huci " kai ina Wallahi ba zaiyu ba sai na dandani zumarki Khadija tabbas sai na sameki". Shi kadai yake magana tamkar da wani yake. A haka ya gama wankan yafito har yanzu Zainab na nan inda ya barta mamaki da alajabin bakon yanayi da suka shiga ita da hyadr take.
Ko kallonta bai ba ya ja bargo ya kwanta, jiki asabule itama ta tashi ta shiga toilet dan tsarkake jikinta. Haka suka kwana babu wani Wanda ya samu bacci mai dadi shi tunaninsa daban itama tunanin ta daban.
(``` wannan shi ake Kira karfin hali barawo da sallama```)
Karfe 10 daidai hydar ya farka daga baccin da yake kasantuwar weekend ne ba aiki shiyasa zainab ba ta tashe shi ba yana tashi wanka ya yi sannan ya yi sallah ya fito cikin shirin fita, Zainab tana zaune tana kallon wani film a zeeworld Hydar ya fito ya yi matukar kyau da kayan da yasa kasuntuwarsa kyakkyzwa ajin farko.
Da murmushi a fuskar zainab ta tashi tana kallonsa tace" Good morning doctor ". Kallonta ya yi ya dan saki murmushi kadan yace "Good morning kin tashi lfy?" Wani murmushi tayi sannan tace" Ba lafiya ba domin doctor na jiya ya sa matarsa cikin damuwa'. Cikin shagwabar da tasan zata burgeshi tayi amma sabanin haka sai ya bata fuska yace" Zaki ban abinci ko sai kin gama surutun?". Cikin sanyi jiki ta saki hannunsa da takama ta yi wajen dinning din, bin bayan ta ya yi da kallo tare da wani gutun tsaki" Mtewwwwww! Yace " Mace sai iyayen tsiya".
0 Comments