💢💢💢```DUHUN JAHILCI💢💢💢



Labari da tsarawa  


     Mamashu  
               
       Da  
       
        Oum sharifa
             
             2effect😘😘😘



```Wannan labari yana kunshe da abubuwan ban mamaki Wanda hankali ko tunani ba zai dauka ba, ko acikin jahilai ba kowa zai aikata irin wannan abun ba  kai ko da dabbobi bane wasu suna sa kishin matansu bare mutum mai hankali Wanda Allah ya sanya masa zuciya da tunani.``` 




``` JARUMAI WRITERS WANNAN SHINE TAKENMU ALKALAMI YAFI TAKOBI```💪🏾💪🏾💪🏾



``` Bismillahir rahmanir rahim ```



```Page 1```


............✍✍✍ Parlor ne mai matukar girma da tsaruwa ,daga ganin masu wannan parlon kasan akwai kudi had'e da jin dadi acikinsa babu wata  hayaniya amma komi a tsare yake cikin nutsuwa da kyau gida ne gidan yan boko Wanda suka amsa sunan su wayayyu.



Hydr yana zaune Kan daya daga lausasan cousin din dake parlon hannusa dauke da waya kirar iPhone 14pro max hankalinsa kwance yana daddannawa. 


Gefen sa kuma Deeni ne Kan computer yana kokarin tura wani email hankalinsa gabadaya yana Kan abunda yake.


Kakkyaywar mace ce tafito daga cikin kitchen hannunta dauke da tire cikin shigar da duk ta bayyana surar jikinta,  bata damu ba domin in da sabo wannan shigar ba komi bace a wajenta, tinda ta fito Hydar ya kura Mata ido babu sassauatawa duk da wannan bashi bane karo na farko da ya fara ganin Khadija, amma yau ganin da ya yi Mata na daban ne tayi masa kyau fiye da duk lokacin da yake ganinta.

Kurrrrrr ya zuba ma kirjinta ido yana kallon yadda suka tsaya kyam acikin breast cut din da ke jikinta, kai kallonsa ya yi zuwa kugunta Wanda ya zauna dass acikin sirkt dinta ga mazaune masha Allah Khadeeja mace ce ta ko ina ta hadu.



Hadiye wani miyau ya yi makut tare da lashe busasssan lebansa ya kuma kara gyara zama yana kallon yadda take shirya abinci akan dinning table din dake dan nesa da su.




Bai dauke idonsa ba har sai da ya ga tagama tana nufu wajen sannan ya yi sauri ya maida kansa kan wayar ,ya cigaba da dannawa wayar amma ta gefen ido ita yake kallo tafiyar ta tamkar tarwada " Ya rabb!" Ya furta a hankali take numfashinsa ya soma daukewa ,shaawar khadija ta  nema waje ta zauna daram a kirjinsa tamkar ya Mike ya rumgumota haka yake ji.



" Dear!' Khadija ta furta a hankali ya yinda ta karasa wajen Deeni da ya maida hankalinsa kan abunda yake bai san duk wainar da ake toya wa ba.



A hankali ya dago idonsa masu matukar kyau ya kalli khadija yace" Wifey yane?" Shagwabe kai tayi alamar nuna gajiya da aikin da yake ta motsa baki tace" Dear ni dai ka bar aikin nan haka kazo muci abinci". Hydr dake zaune yana kallon abunda khadija take take wani shauki ya cigaba da azalzalarsa tamkar ya rumgumeta ya tsotsi bakinta mai matukar kyau da tsari da daukar hankalin duk wani namiji mai cikakkiyar lafiya.


Murmushi Deeni ya saki tare da dan rungumo kugunta yace " Muje ko An babyna" itama murmushin ta saki tare da kama sajen dake kwance Kan kakkyawar fuskar mijin nata tace " Ko kaifa". Mikewa yayi tare da kallon in da Hdyar yake yace " Oya madam ta hana aiki muje muci abinci". Murmushin kan labba hydar ya yi tare da mikewa cikin kasala ya bi bayan su.


Khadija ce ta zuba musu abinci sannan itama ta zauna ta zuba nata hankalinta kwance shima Deeni haka, ban da Hydar da ya kasa nutsuwa ya ci
abincin idonsa yana kan Khadija dake cin abincinta.

Dago kai Khadija tayi ganin kamar ana kallon ta,idonta sauka ya yi kan Hydr da zuba Mata idonsa yana kallonta sakin murmushi tayi cikin rashin damuwa da irin kallon da yake Mata tace"Ya dai ko abinci bai dadi bane naga ka zuba min ido kana kallona?" Ta tambya tana kallonsa kurrrr ido cikin ido.



Sauke numfashi Hydar ya yi ya furta  a hankali" Kina da kyau khadija". " Me kace?" Ta kuma tambya dariya ya yi tare da shafa gemunsa  sannan yace " Ina ni ina cewa gimbiyar Mata kuma sarauniyar kyawawa ta duniya bata iya girkiba?" Girkinan ko a aljanna na sameshi ai nagama morewa". 




"Laaaaaaaaaaaaa! Dear kaji tsiya ko wajen Hydar"? Ta fada tana guntse yar karamar dariya tana kallon mijinta" Deeni kuwa sai cewa ya yi " Ita ku ni ba zan shiga tsakaninku ba.". Duka sai suka sa dariya.




A haka suka gama cin abinci ya yinda rabin hirar Khadija da Hydar keyi shi kuma Deeni Yana dube dube kan wayarsa yana cin abincin. Sai da suka gama Khadija ta kwashe kayan tayi kitchen,su kuma suka koma wajen zaman su.



Hydar ne ya kalli Deeni yace " Kai mutumina amma fa ka more Mata wallahi". Dariya Deeni ya yi yace " Haba dai wani na more Mata zolaya ta dai kake". Dariya Hydar ya yi yace " Wallahi fa da gaske nake matarka itace irin macen da nake da burin aure Wallahi sai gashi Kaine ka samu ba ni ba". Wata dariyar Deeni ya yi cikin rashin kishin abunda Hydar ya fada yace " Allah mutumina kace na more mace alaji". Dariya Hydar ya kuma yi yace " Ina gayama fa komi matarka taji fa komi sambarka kamar kaban aro". Duka Deeni ya kai masa yace " Aron wa din zan baka?" "Khadija mana" Hydar ya bashi amsa.




" A................kirr kirr wayar Hydar ta yi ringing shine abunda ya katse Deeni daga magana Hydar ne ya Mike cikin sauri yace " Ok I'm coming in sha Allah ". Sannan ya kashe wayar yana kallon Deeni yace " Kira da ga asibiti ina da aikin gaggawa bara na tafi". Mikewa Deeni ya yi sannan ya mika masa hannu yace " Ok sai munyi waya. 
Da sauri Hydr ya fito daga cikin parlon ya dauki matarsa ya yi asibiti.


Bai gama aikin da yake ba sai karfe 10pm sannan ya fito cikin matukar gajiya ga tsananin shaawar dake addabarsa tin barin gidan amininsa, cire kayan aikin ya yi ya je ya dauki brief case dinsa ya nufi gida

Horn ya yi mai gadi ya bude masa ya shiga ya yi parking sannan ya shiga cikin gidan cikin tsananin gajiya.


Zainab na zaune kan daya daga cikin kujeran dakin tasha kwalliyarta tamkar mai shirin shiga gasar kyawawa ta duniya mace mai matukar kyau da tsari domin zan iya cewa har tafi khadija kyau banbancin kawai ita bata da tsayi amma cikakkiyar mace mai kyau da kyawun siffa.



A hankali ta taso tayi wajensa cike da murmushi a fuskarta ta karbi jakarsa, siririn tsaki ya saki tare da dan bata fuska ya kalleta yace " Wannan wace irin kwalliya ce haka kin wani cika jan baki?" Kallonsa ta yi cikin mamakin maganar sa tace" Me kwalliya ta yi kuma?". " Gani nayi baki yi kyau kamar Khadija ba". " Khadeeeja!" Zainab ta ja sunanan wacece kuma Khadija?" Ta tambya cike da mamaki. Saurin ankara  yayi da katobarar da ya yi yace " Uhm ba kowa muje ciki yar matata wasa nake miki fa". Bata fuska tayi hade da yar karamar harara tace" Ni dai ban yarda ba ko kanwa zaka min?" Murmushin takaici ya yi da ya ga yadda tayi duk da tayi matukar kyau amma bai ga kyan ba zuciyarsa tana ga wace shaidan ya kada masa ganga yace" Ke ban son tabara  muje ciki nagaji wanka zanyi, yana fadar haka ya shige bedroom dinsa.



Bin bayansa tayi hannunta dauke da jakar shi bayan ta ajiye ta fito dan hada masa abinci, sai da ya yi sallah ya fito ya zo ya sameta tana jiransa, kallo ya zuba Mata irin kallon kurillah take fuskar Khadija ta bayyana a Kan fuskar zainab. Cikin sassasarfa ya isa Kan dinning din ya kama hannun zainab yace " Kema kina jin irin abunda nake ji kanki ko? Tabbas sai na sameki Wallahi ina matukar shaawarki kh.......................




```` Somin tabi wai ango ya taba nono ku biyomu dan jin wannan tsakwakiyar mai cike da hadarin gaskke```



```Daga takasar matasan marubuta mamashu tare da oum sharifa```




``` comment and share pisabillah```



```Garkuwarku ce tare da shalelen ku```😘😘😘